Mummunar fashewar bututun gas ya janyo tashin hankali a garuruwan Bayelsa

Mummunar fashewar bututun gas ya janyo tashin hankali a garuruwan Bayelsa

An nemi wasu mutane da dama an rasa a garuruwan Nembe da Jalungo fa Fatuo da Kalablomi sakamakon fashewar bututun iskar gas daga bututun gas na garin Nembe da kamfanin Aiteo ke kula dashi a safiyar yau.

An gano cewa fashewar gas din da ya afku a safiyar yau Juma'a ya janyo hargitsi da tashin hankula a garuruwan Nembe.

Bututun gas din ya kama da wuta ne misalin karfe hudu na asubahi kusa da rijiyar man mai lamba 7 hakan ya jefa mazauna garin da wadanda ke makwabtaka da su a cikin ruduni inda har yanzu ana neman wasu ba a gansu ba.

Mummunar fashewar bututun gas ya janyo tashin hankali a garuruwan Bayelsa
Mummunar fashewar bututun gas ya janyo tashin hankali a garuruwan Bayelsa
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Yadda Buhari ya yi murdiyya wajen lashe zaben 2019 - Sheikh Ahmad Gumi

Wani mazaunin garin mai suna Patrick ya shaidawa manema labarai cewa fashewar bututun gas din ya gurbuta iska da ruwa a garuruwan wanda hakan ya janyo masunta sun dena kamun kifi.

Mai magana da yawun fadar sarkin Nembe, Cif Nengi James Eriworio ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce hakan ya janyo "gurbacewar iska da ruwa a garin."

A cewar Cif James-Eriworio, "mutane da dama sun tsere daga gidajensu kuma kamfanin da gaza zuwa da gyara bututun iskar gas din duk da cewa an kira su cikin gaggawa.

"Misalin karfe 6 na yamma, a lokacin da ke ke kira, wuta tana nan tana ci. Wannan abu ne da ya faru saboda sakaci kuma abin tambaya ne. Mutane sun razana. Mata da yara da yawa sun bata."

Ya yi kira ga kamfanonin da ke hakar mai a yankin su kula da walwalar al'ummar yankin kuma ya bukaci hukumomin gwamnati su kawo wa al'ummar garin dauki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel