Ba'a taba sahihin zabe ba a Najeriya kamar na 2019 inji wani basaraken kudu

Ba'a taba sahihin zabe ba a Najeriya kamar na 2019 inji wani basaraken kudu

Wani basaraken masarautar kasar Benin Cif David Edebiri a jiya ya bayyana cewa zaben tazarcen shugaba Muhammadu Buhari da ya gudana a ranar Asabar din karshen watan Febreiru ba'a taba yin wanda ya kai shi sahihanci ba tun da aka kirkiri Najeriya.

Haka ma kuma Cif David Edebiri ya shawarci dan takarar shugaban kasar a jam'iyyar adawa ta PDP, Alhaji Atiku Abubakar da ya rungumi kaddara ya karbi sakamakon zaben ya kuma hada hannu da shugaba Buhari wajen ciyar da kasar nan gaba.

Ba'a taba sahihin zabe ba a Najeriya kamar na 2019 inji wani basaraken kudu
Ba'a taba sahihin zabe ba a Najeriya kamar na 2019 inji wani basaraken kudu
Asali: UGC

KU KARANTA: Yan bindiga sun kai sabon farmaki Zamfara

Legit.ng Hausa ta samu cewa Basaraken ya bayyana cewa tun zaben Najeriya na farko a shekarar 1951 yakeyin zabe kuma har zaben da ya gabata ma yayi amma shi a bisa dukkan alamun yadda yaga zaben, ba'a taba yin tsaftataccen zabe kamar sa ba.

A wani labarin kuma, Hukumar shirya zabe mai zaman kanta ta kasa watau Independent National Electoral Commisslon (INEC) ta bada labarin cewa an yi zina da wasu ma'aikatan ta mata a yayin zabukan da aka gudanar satin da ya gabata na shugaban kasa da 'yan majalisar wakilai.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da babban jami'in yada labarai da wayar da kan masu zabe na hukumar Mista Festus Okoye ya fitar dauke da sa hannun sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel