Buhari ya gana da kwamitin zaman lafiya a Aso Rock

Buhari ya gana da kwamitin zaman lafiya a Aso Rock

Kasa da sa’o’i 24 bayan ganawa da Atiku Abubakar, dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), a yanzu haka kwamitin zaman lafiya na cikin ganawa makamanciyar hakan tare da Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

An gudanar da ganawar sirrin ne tare da Buhari a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa an fara ganawar ne da misalign karfe 3:00 na rana a ofishin Shugaban kasa.

Wadanda suka halarci ganawar sun hada da tsohon Shugaban kasa, Abdulsalami Abubakar, babban limamin coci na Sokoto, Hassan Matthew Kukah, da kuma Cardinal John Onaiyekan.

An tattaro cewa shugaban jamíyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Adams Oshiomhole ma na wajen.

A baya mun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP da ya sha kaye a zaben 2019, Atiku Abubakar ya gabbatar da wasu muhimman bukatu 5 da ya ke so daga gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Hukumar INEC ta shirya yin zabe a wuraren da ba a gudanar da zabe ba

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya gabatar da bukatun ne a yayin ganawarsa da wata tawaga daga kwamitin zaman lafiya na kasa (NPC) karkashin jagorancin Janar Abdulsalami Abubakar (mai murabus) kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Legit.ng ta gano cewa Atiku Abubakar ya yi gargadin cewa hankulan mutane yana tashi a halin yanzu a yayin ganawarsa da Abdulsami tare da abokin takararsa Peter Obi da sauran jiga-jigan jam'iyyar PDP.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel