Da duminsa: Mata sun mamaye Abuja, sun bukaci Atiku ya amince da shan kaye

Da duminsa: Mata sun mamaye Abuja, sun bukaci Atiku ya amince da shan kaye

- Wata kungiyar mata ta roki Atiku Abubakar da ya taya shugaban kasa Buhari na jam'iyyar APC murnar lashe zabe tare da amince da shan kaye

- Sun yi kira ga Atiku da ya bi sahun tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan tare da taya Buhari murnar lashe zaben shugaban kasar a karo na biyu

- Matan sun kuma yi kira ga Buhari da kar ya baiwa 'yan Nigeria kunya wadanda suka fito kwansu da kwarkwatarsu domin zabensa a karo na biyu

Wata kungiyar mata, karkashin kungiyar gangamin mata miliyan 2 domin demokaradiyya a Nigeria, a ranar Juma'a ta roki Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP a zaben ranar Asabar da ya gudana da ya taya shugaban kasa Buhari na jam'iyyar APC murnar lashe zabe tare da amince da shan kaye.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana shugaban kasa Buhari na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben da tazara mai yawa a zaben ranar Asabar da ta gabata.

Sai dai, Atiku ya sha alwashin daukaka kara zuwa kotu, yana mai cewa an tafka magudi a zaben.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Okorocha, Amosun na fuskantar kalubale, APC za ta kore su gaba daya

Da duminsa: Mata sun mamaye Abuja, sun bukaci Atiku ya amince da shan kaye
Da duminsa: Mata sun mamaye Abuja, sun bukaci Atiku ya amince da shan kaye
Asali: Facebook

Matan sun fara zanga-zangarsu ne daga Unity Fountain down har zuwa Hilton bayan da suka garzaya shelkwatar rundunar tsaro, zuwa babban filin taro na Eagle Square kana suka dawo Unity Fountain.

Sun yi kira ga Atiku da ya bi sahun tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan tare da taya Buhari murnar lashe zaben shugaban kasar a karo na biyu.

Da ta ke jawabi a wajen gangamin, wacce ke jagorantar kungiyar, Mary Onuche, ta yi kira ga Atiku da ya ceci Nigeria daga shiga rudani tare da rungumar dan uwansa Buhari.

Onuche ta kuma yi kira ga Buhari da kar ya baiwa 'yan Nigeria kunya wadanda suka fito kwansu da kwarkwatarsu domin zabensa a karo na biyu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel