Sabon zababben dan majalisa ya bukaci Buhari da ya jagoranci APC wajen zabar shugabannin majalisa

Sabon zababben dan majalisa ya bukaci Buhari da ya jagoranci APC wajen zabar shugabannin majalisa

Sabon zababben dan majalisa ya bukaci Buhari da ya jagoranci APC wajen zabar shugabannin majalisa

Ahmed Manir, wani sabon zabebben dan majalisar wakilai mai wakiltan mazabar Lere, yayi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya jagoranci APC wajen zabar shugabannin majalisun dokoki.

Ya jadadda cewa kada Shugaba Buhari ya bari mutane masu son zuciya su karbe majalisar dokokin kamar yadda suka yi a 2015.

Sabon zababben dan majalisa ya bukaci Buhari da ya jagoranci APC wajen zabar shugabannin majalisa
Sabon zababben dan majalisa ya bukaci Buhari da ya jagoranci APC wajen zabar shugabannin majalisa
Asali: UGC

Sabon dan majalisar ya bayyana cewa ya rigada ya tabbata cewa APC ce ke da mafi rinjaye a majalisar dattawa da na wakilai duba ga sakamakon da hukumar zabe mai zaman kanta ta saki.

Da farko Legit.ng ta rahoto cewa yayinda APC ta kafa mafi rinjaye a majalisar dattawa, akalla sanatoci masu ci 64 da mambobin majalisar wakilai 151 ne ba za su dawo majalisar dokokin kasaar ba a raanar 9 ga watan Yuni da za a rantsar da sabbin shiga.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Gwamnatina zai yi zafi sosai a wannan karon – Buhari

Sanatoci 45 kawai ne da kimanin mambobin majalisar wakilai 209 ne za su dawo majalisar tarayyar kasar. 15 daga cikin sababbin sanatocin da aka zaba sun kasance tsoffin gwamnonin jiha.

42 daga cikin sanatoci 64 da ba za su dawo ba sun rasa kujerarsu ne tun a watan Oktobar shekarar da ta gabata a zaben fidda gwanin jam’iyyunsu.

Sauran 22 sun sha kaye ne a zaben majalisar dokoki da ya gudana a ranar Asabar da ya gabata.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel