Da duminsa: Okorocha, Amosun na fuskantar kalubale, APC za ta kore su gaba daya

Da duminsa: Okorocha, Amosun na fuskantar kalubale, APC za ta kore su gaba daya

Rahotannin da Legit.ng Hausa ke samu yanzu na nuni da cewa kwamitin ayyuka na jam'iyyar APC na kasa ya dakatar da gwamnan jihar Ogun Ibikunle Amosun da takwaransa na jihar Imo, Rochas Okorocha daga jam'iyyar.

Jaridar TheCable ta ruwaito cewa, kwamitin NWC na APC ya gabatar da wata bukata ga kwamitin zartaswa na jam'iyyar na kasa, na duba yiyuwar korar gwamnonin biyu daga jam'iyyar gaba daya.

Kwamitin NWC na APC ya dauki wannan matakin ne a wani taro da ya gabatar a ranar Juma'a a Abuja inda kwamitin ya bayyana cewa sun yanke hukuncin ne biyo bayan yiwa jam'iyyar zagon kasa da gwamnonin suke yi.

KARANTA WANNAN: Kotu: Wasu manyan jami'an gwamnatin Akwa Ibom guda 4 sun shiga tsaka mai wuya

Da duminsa: Okorocha, Amosun na fuskantar kalubale, APC za ta kore su gaba daya
Da duminsa: Okorocha, Amosun na fuskantar kalubale, APC za ta kore su gaba daya
Asali: UGC

An dai zabi Amosun da Okorocha zuwa majalisar dattijai karkashin jam'iyyar APC a zaben ranar Asabar da aka gudanar amma suna goyon bayan 'yan takarar gwamnonin jihohinsu a wasu jam'iyyun daban, a zaben gwamnoni da za a gudanar ranar 9 ga watan Maris.

Cikakken labarin na zuwa...

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel