Kotu: Wasu manyan jami'an gwamnatin Akwa Ibom guda 4 sun shiga tsaka mai wuya

Kotu: Wasu manyan jami'an gwamnatin Akwa Ibom guda 4 sun shiga tsaka mai wuya

Wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke da zama a Legas ta amince da cafke Antoni Janar kuma kwamishinan shari'a na jihar Akwa Ibom, Uwemedimo Nwoko, da kwamishinan kudi, Nsikan Nkan, da babban akawu, Mfon Udomah da kuma kashiyar gwamnatin jihar, Margaret Ukpe.

Mai shari'a Rilwan Aikawa ya bayar da umurnin cafke manyan jami'an gwamnatin bisa bukatar da hukumar EFCC ta gabatarwa kotun, bayan sanar da kotun cewa cafke jami'an gwamnatin ya zama wajibi domin tabbatar da cewa sun gurfana gaban kotu a zaman kotun na ranar 18 da 19 ga watan Maris, 2019.

Ana zargin manyan jami'an gwamnatin guda hudu tare da shugaban kungiyar lauyoyi ta kasa, Paul Usoro da aikata laifukja 10 da suka hada da cin amanar kasar da kuma karkakatar da N1.4bn da aka ce mallakin gwamnatin jihar ne, wajen aiwatar da wasu ayyuka ba a hukumance ba.

KARANTA WANNAN: Babbar magana: APC ta bukaci INEC ta sake gudanar da zabe a mazabar Dogara

Kotu: Wasu manyan jami'an gwamnatin Akwa Ibom guda 4 sun shiga tsaka mai wuya
Kotu: Wasu manyan jami'an gwamnatin Akwa Ibom guda 4 sun shiga tsaka mai wuya
Asali: Depositphotos

Rahotanni sun bayyana cewa sun aikata laifukan da ake zarginsu ne a cikin watan Mayun 2016.

Sai dai Mr Usoro ya karyata wannan zargi da ake yi masa, da wannan ne kuma aka bayar da belinsa akan kudi N250.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel