FG za ta kafa masana'antar kera kayan jami'an tsaro

FG za ta kafa masana'antar kera kayan jami'an tsaro

Gwamnatin tarayya ta ce ta kammala shiri domin kafa masana'antar sarrafa tufafi domin amfanin sojoji da sauran hukumomin tsaro a Kaduna domin rage dogaro ga kayayakin kasashen waje.

A jiya ne aka gabatarwa Ministan tsaro, Mansur Dan Ali cikaken takardun izinin kafa masana'antar da za a gina a Kaduna.

A yayin da ya ke gabatar da takardan izinin ga ministan, shugaban hukumar kula da gine-gine ICRC, Chidi Izuwa ya ce kamfanin da za a bukaci Naira Biliyan 4 wurin gininsa zai fara zai rika samar wa gwamnati kudin shiga bayan ya fara aiki.

Gwamnati za ta kafa masana'antar sarrafa kayan sojoji a Kaduna
Gwamnati za ta kafa masana'antar sarrafa kayan sojoji a Kaduna
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Karkatar da kudin makamai: Tsohon Sojan Saman Najeriya zai yi shekaru 7 a kurkuku

Ya ce masana'antar hadin gwiwa ce tsakanin Masana'antar Kera makamai ta Najeriya (DICON) da Sue Corporate Wear kuma za ta fara aiki cikin watanni takwas zuwa shekara guda.

A jawabin da ya yi a baya, shugaban DICON, Manjo Janar B.O. Ogunkale ya ce masana'antar za ta samar da ayyuka ga mutane 1,300 idan an fara aiki inda ya kara da cewa suna bukatar Naira Miliyan 100 a mastsayin jari.

Ya ce za a rika raba riba ne dai-dai tsakanin DICON da Sur Corporate.

A jawabinsa, Ministan Tsaro na Najeriya, Mansur Dan Ali ya yi juyayin yadda Najeriya ta dogara da sayen makamai daga kasahen waje har ma da kayan sojoji na tsawon shekaru masu yawa.

Ya ce samun izinin kafa masana'antar babban cigaba ne da zai kawo canji a Najeriya musamman saboda za su samu daman samarwa sojoji bukatunsu.

Ya ce masana'antar za ta samarwa sojoji da kayan sawa da ma wasu bukatunsu na daban.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel