Yanzu Yanzu: Gwamnatina zai yi zafi sosai a wannan karon – Buhari

Yanzu Yanzu: Gwamnatina zai yi zafi sosai a wannan karon – Buhari

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari a ranar Juma’a, 1 ga watan Maris ya bayar da karin haske akan yadda mulkinsa na biyu zai kasance. Ya kaddamar da cewa zai yi zafi a wannan karon.

Shugaban kasar wanda ya lashe zabe a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), yayi jawabi lokacin day an majalisarsa suka kai masa ziyarar taya murna.

Daily Trust ta ruwaito inda yake cewa wa’adin karshe na gwamnatinsa zai yi zafi sosai.

Yanzu Yanzu: Gwamnatina zai yi zafi sosai a wannan karon – Buhari
Yanzu Yanzu: Gwamnatina zai yi zafi sosai a wannan karon – Buhari
Asali: Facebook

“Shekaru hudun da zanyi na karshe, ina ganin zai yi zafi. Mutane na da mantuwa sosai shiyasa a lokacin kamfen nayi Magana akan ajandarmu,” inji shi.

Jaridar The Nation ta ruwaito inda Shugaban kasar ke cewa zai jajirce ta fanoni uku da suka shafi tsaro, tattalin arziki da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

Buhari ya fada ma bakin cewa yayi kamfen a fadin jihohi 36 na tarayyar kasar harda babbar birnin tarayya domin ya tabbatar da cewa yana da karfin jiki da lafiyar ci gaba da mulki.

Babban sakataren tarayya, Boss Mustapha wanda yayi Magana a madadin sauran jami’an gwamnati, ya taya Shugaban kasar da mataimakinsa, Yemi Osinbajo murna akan nasarar da suka yi a zaben kasar.

Mustapha yace Shugaban kasar ya cancanci yin nasara saboda gaskiyarsa da amana.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel