Babbar magana: APC ta bukaci INEC ta sake gudanar da zabe a mazabar Dogara

Babbar magana: APC ta bukaci INEC ta sake gudanar da zabe a mazabar Dogara

- Jam'iyyar APC ta bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da ta sake gudanar da sabon zabe a mazabar Bogoro/Dass/Tafawa Balewa

- APC ta ce ta yi fatali da sakamakon zaben wanda Yakubu Dogara ya lashe, sakamakon kura kuran da aka tafka a cikinsa

- Haka zalika jam'iyyar ta yi ikirarin cewa an yi awon gaba da wasu daga cikin jami'anta, inda aka sake su bayan an kammala zaben

Jam'iyyar APC ta bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da ta sake gudanar da sabon zabe a mazabar Bogoro/Dass/Tafawa Balewa, jihar Bauchi, mazabar da kakakin majalisar wakilan tarayya, Yakubu Dogara ke wakilata a majalisar wakilan tarayyar.

Jam'iyyar ta yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa daga hannun shugaban kwamitin wata labarai da harkokin jama'a na ofishin yakin zaben APC a jihar, Balarabe Shehu Illelah.

APC ta bayyana cewa, ta yi fatali da sakamakon zaben kujerar majalisar wakilan tarayya na mazabar ne, wanda aka bayyana Yakubu Dogara a matsayin wanda ya lashe zaben, sakamakon kura kuran da aka tafka a cikinsa.

KARANTA WANNA: Da duminsa: Kotun daukaka kara ta kafa kwamitin sauraron korafe korafen zabe

Babbar magana: APC ta bukaci INEC ta sake gudanar da zabe a mazabar Dogara
Babbar magana: APC ta bukaci INEC ta sake gudanar da zabe a mazabar Dogara
Asali: Twitter

A cewar sanarwar, biyo bayan kura kurai da karya dokokin zabe da aka yi a zaben mazabar, ya zama wajibi ta bukaci INEC ta sake gudanar da sabon zabe.

Haka zalika jam'iyyar ta yi ikirarin cewa an yi awon gaba da wasu daga cikin jami'anta, inda aka sake su bayan an kammala zaben, yayin da aka kaiwa wasu farmaki tare da lalata ababen hawansu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel