Da duminsa: Kotun daukaka kara ta kafa kwamitin sauraron korafe korafen zabe

Da duminsa: Kotun daukaka kara ta kafa kwamitin sauraron korafe korafen zabe

- Mai shari'a Zainab Bulkachuwa, ta kafa wani kwamiti da zai saurari korafe korafe kan zaben zaben 2019 a na jihar Jigawa

- Za ayi amfani da babban dakin sauraron kara na babbar kotun majistire ta 1, da ke cikin babbar kotin shari'a ta Duste, a matsayin kotun sauraron korafe korafen

- Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a garin Dutse a ranar Alhamis

Shugabar babbar kotun daukaka kara ta gwamnatin tarayya, mai shari'a Zainab Bulkachuwa, ta kafa wani kwamiti da zai saurari korafe korafe kan zaben gwamnoni, yan majalisun dokoki da na tarayya a zaben 2019 a na jihar Jigawa.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a garin Dutse a ranar Alhamis.

KARANTA WANNAN: Gaskiyar magana: Ni fa ban ci kudin yakin zaben PDP a 2015 ba - Belgore

Da duminsa: Kotun daukaka kara ta kafa kwamitin sauraron korafe korafen zabe
Da duminsa: Kotun daukaka kara ta kafa kwamitin sauraron korafe korafen zabe
Asali: Depositphotos

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, ya ruwaito cewa babban joji na jihar, mai shari'a Aminu Sabo, ta hanyar wannan sanarwa, ya amince da yin amfani da babban dakin sauraron kara na babbar kotun majistire ta 1, da ke cikin babbar kotin shari'a ta Duste, a matsayin kotun sauraron korafe korafen.

Sanarwar ta bukaci hukumomin tsaro da suka hada da rundunar 'yan sanda, hukumar tsaro ta farin kaya (SSS), 'yan Jaridu da kuma daukacin al'umma da su sani cewa za a fara rejistar korafe korafen ne da misalin karfe 8 na safiyar kowacce rana.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel