Nasarar cin zabe: Kungiyar kasashen nahiyar Afirka gaba daya ta taya Buhari murna

Nasarar cin zabe: Kungiyar kasashen nahiyar Afirka gaba daya ta taya Buhari murna

Hadaddiyar kungiyar kasashen nahiyar Afirka kwata, AU, ta fitar da sanarwar taya shugaban kasa Muhammadu Buhari murnar lashe zaben shugaban kasar Najeriya daya gudana a ranar Asabar, 23 ga watan Feburairu.

Legit.ng ta ruwaito shugaban kungiyar AUM, Moussa Faki Mahamat ne ya sanar da cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin hukumar na yanar gizo, inda yace kungiyar ta yaba da yadda aka gudanar da zaben shugaban kasa da nay an majalisu a Najeriya.

KU KARANTA: Jami’ai sun tashi dandalin shan wiwi 45, tare da cafke mashaya 250 a Kano

Nasarar cin zabe: Kungiyar kasashen nahiyar Afirka gaba daya ta taya Buhari murna
Buhari
Asali: UGC

“Sakamakon sanarwar da hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta fitar a ranar 27 ga watan Feburairu, inda ta sanar da shugaba Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben, don haka muke tayashi murnar samun nasara.

“Haka zalika kungiyar na yi ma shugaban kasa Buhari da sauran yan Najeriya fatan yin zabe na gaba lafiya, tare da gina da kasa mai cike da zaman lafiya, kwanciyar hankali da kuma karin arziki.” Inji shi.

Shugaban kungiyar, Mahamat ya bayyana cewa rahoton da kwamitin AU na sa’ido a zaben Najeriya ta bayar ya tabbatar da sahihanci tare da ingancin zaben da aka gudanar a Najeriya, wanda yace ya dace da dokokin kasar.

Shugaban hukumar AU ya bayyana cewa zaben da aka gudanar wani mataki ne da zai jaddada Najeriya akan turbar Dimukradiyya, sa’annan ya yaba ma hukumar zaben Najeriya, INEC bisa zaben adalci da gaskiya da gaskiya da ta shirya.

A wani labarin kuma, tun bayan nasarar da shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya samu a babban zaben kasar inda ya kayar da babban abokin hamayyarsa a zaben shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, kasashen duniya keta rige rigen tayashi murna.

Kasa ta farko data fara taya shugaba Buhari murnar samun nasara itace kasar China, inda shugaban kasar China, Xi Jin Ping ta bakin kaakakin ma’aikatan kula da harkokin kasashen Afirka ta kasar, Lu Kang ya taya Buhari murnar samun nasara, inda yace China na ganin girman Najeriya matuka.

Sauran shuwagabannin kasar sun hada da Nana Akufo Addo na Ghana, Emmerson Manangwagwa na Zimbabwe, Macky Sall na kasar Senegal, Mahamadou Issoufou na Nijar, Sarki Mohammed Hassan na Morocco, Alpha Conde na Guinea, Theresa May ta Birtaniya, Donald Trump na Amurka, Uhuru Kenyatta na kasar Kenya da Cyril Ramaphosa na Afirka ta kudu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel