Yanzu Yanzu: Hukumar INEC ta shirya yin zabe a wuraren da ba a gudanar da zabe ba

Yanzu Yanzu: Hukumar INEC ta shirya yin zabe a wuraren da ba a gudanar da zabe ba

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) za ta gudanar da zabe a yankunan da ba a gudanar da zabe ba a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu.

Zaben zai gudana ne a ranar 9 ga watan Maris, tare da na gwamnoni, da majalisun jiha da kuma na birnin tarayya.

Baya ga haka, hukumar ta umurci kwamishinonin zabe na jiha da su gabatar da rahoto akan lamarin rikici da ya afku ga hukumar domin daukar matakin da ya kamata.

Yanzu Yanzu: Hukumar INEC ta shirya yin zabe a wuraren da ba a gudanar da zabe ba
Yanzu Yanzu: Hukumar INEC ta shirya yin zabe a wuraren da ba a gudanar da zabe ba
Asali: UGC

An kai wannan matsayar ne a ganawar da ya gudana tsakanin manyan jami’an INEC da kuma kwamishinonin zabe na jihohi 26 da kuma birnin tarayya.

KU KARANTA KUMA: Kasar Ingila ta tabbatar da ingancin sakamakon zaben Najeriya

A baya Legit.ng ta rahoto cewa akwai alamun cewa wasu kwamishinonin zabe ma jiha da kwamishinonin zabe na kasa daga hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) za su yi murabus daga matsayinsu biyo bayan zargin barazana da tozarci da kuma barazanar da rayuwarsu ta samu daga hukumomin tsaro a lokacin zaben Shugaban kasa da na majalisa da ya gudana a ranar 23 ga watan Fabrairu.

Kwamishinonin zabe na jiha da na kasa sun yi zargin cewa sun kasance masu dakiya da duba ga Shugaban hukumar kan tarin hatsarin da rayuwarsu ke ciki sai dai sun kasa hakan saboda shima kansa yana fuskantar tarin matsi da yawan hare-hare daga manyan mutane.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel