Kasar Ingila ta tabbatar da ingancin sakamakon zaben Najeriya

Kasar Ingila ta tabbatar da ingancin sakamakon zaben Najeriya

Kasar Ingila ta tabbatar da sakamakon zaben shugaban kasa da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana a matsayin mai inganci.

Ministar kasar mai kula da hulda da Afirka, Harriet Baldwin, ta ce sakamakon zaben yayi daidai da sakamakon da wata kungiya mai zaman kanta wato civil society Parallel Vote Tabulation process ta samu.

Shugaban hukumar INEC Mahmood Yakubu, a safiyar Laraba, ya bayyana shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben 23 ga watan Fabrairu, inda ya samu kuri’u 15,191,847.

Babban abokin adawansa, Atiku Abubakar na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya samu kuri’u 11,262,977.

Kasar Ingila ta tabbatar da ingancin sakamakon zaben Najeriya
Kasar Ingila ta tabbatar da ingancin sakamakon zaben Najeriya
Asali: UGC

Amman wakilin jam’iyyar PDP a inda ake hada kuri’u ya ki sa hannu a takardan sakamakon sannan Atiku ya ki amincewa da sakamakon inda yace zai kalubalanci sakamakon a kotu.

A wani taro na manema labarai a ranar Laraba, Atiku ya karfafa rashin kin amincewa tare da nuni kan yanayin kididdiga a sakamakon wasu jihohin kasar.

Jawabin da Ministan Birtaniyan tayi ya kasance inganci na farko kan sakamakon hukumar INEC.

Baldwin ta taya shugaban kasa Muhammadu Buhari murnar lashe zaben shugaban kasa a karo na biyu. TYa kuma yabi Yan Najeriya bisa jajircewarsu ga damokardiyya.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya gana da Bakare a fadar Shugaban kasa

Har ila yau, ta saurari damuwar da yan Najeriya suka bayyana akan yanayin gudanar da zabe, musamman dabaru da hade haden sakamako da rahotanni dake nuna razana jami’in zabe

Minstan Birtaniyan ta bukaci duk jam’iyya dake da nufin kalubalantar skamakon zabe da su yi hakan cikin zaman lafiya ta hanyar da ya dace.

Baldwin ta kuma yi jaje ga iyalai da abokan wadanda suka rasa rayukansu a rikicin zabe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel