Gaskiyar magana: Ni fa ban ci kudin yakin zaben PDP a 2015 ba - Belgore

Gaskiyar magana: Ni fa ban ci kudin yakin zaben PDP a 2015 ba - Belgore

- Mai shari'a Rilwan Aikawa na babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Legas ya dage sauraron shari'ar Belgore, SAN, har zuwa ranar 5 ga watan Maris, 2019

- An gurfanar da Belgore gaban kotun ne bisa zarginsa da karbar N450m daga cikin $115,010,000 da Diezani Alison-Madueke ta raba domin murde zaben 2015

- Sai dai Belgore ya ce ba tun yau ba, ya sha gabatar da jawabai a 2016 da 2017 kan cewar bai karbi wadannan kudade da ake zargin ya karba ba

Mai shari'a Rilwan Aikawa na babbar kotun gwamnatin tarayya da ke da zama a garin Ikoyi, jihar Legas ya dage sauraron shari'ar Muhammad Dele Belgore, SAN, har zuwa ranar 5 ga watan Maris, 2019.

An gurfanar da Belgore gaban kotun ne tare da wani tsohon ministan tsare tsaren kasa, Farfesa Abubakar Sulaiman, bisa zarginsu da karbar N450m a ranar 27 ga watan Maris, 2015 daga cikin $115,010,000 da tsohuwar ministar albarkatun man fetur, Diezani Alison-Madueke ta sanya a asusun bankin Fedelity domin murde zaben 2015 don baiwa PDP nasara.

A zaman karshe na kotun da aka dage a ranar 11 ga watan Fabreru 2019 a lokacin da Belgore ya fara gabatar da shaidun kariyarsa, ya shaidawa kotun cewa bai karbi kudin da ake zarginsa da karba ba.

KARANTA WANNAN: Dr Felix: Wanda ya zo na 3 a zaben shugaban kasa ya yiwa 'yan Nigeria godiya

Gaskiyar magana: Ni fa ban ci kudin yakin zaben PDP a 2015 ba - Belgore
Gaskiyar magana: Ni fa ban ci kudin yakin zaben PDP a 2015 ba - Belgore
Asali: UGC

Haka zalika, mai shari'ar ya dage shari'ar zuwa yau domin baiwa dukkanin bangarorin damar kallon hotuna masu motsi da na'urar daukar hoton sirri (CCTV) ta dauka, inda wanda ake zargin ya ziyarci bankin domin karbar kudin.

A yayin zaman kotun na yau, an kunna bidiyon domin kowa ya kalla. Inda daga bisani, Belgore ya shaidawa kotun cewa duk da ya kalli bidiyon da bankin Fedelity, reshen Ilorin ya gabatar, inda a cikinsa aka nuna shi yana karbar kudin, yana da bukatar ya yi nazari kan bidiyon domin bai aminta da ingancinsa ba.

Da wannan, mai shari'ar ya bayyana bidiyon da takardunsa a matsayin shaida ta 12 da 12A.

Belgore ya ce ba tun yanzu ba, ya sha gabatar da jawabai a tsakanin watan Nuwamba 2016 da watan Fabreru, 2017 kan cewar bai karbi wadannan kudade da ake zargin ya karba ba.

Da wannan, mai shari'a Aikawa, ya dage sauraron karar har zuwa ranar 5 ga watan Maris, 2019 domin ci gaba da sauraron karar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel