Buhari ya gana da Bakare a fadar Shugaban kasa

Buhari ya gana da Bakare a fadar Shugaban kasa

- Fasto Tunde Bakare ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa

- Limamin cocin bai yi jawabi ga manema labarai ba bayan ganawar tasu

- Bakare ya kasance abokin takarar Buhari a zaben 2011

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da babban limamin cocin Latter Rain Assembly (LRA), Fasto Tunde Bakare, jiya Alhamis, 28 ga watan Fabrairu a fadar shugaban kasa.

A cewar jaridar Leadership, ziyarar na iya samun nasaba da nasarar Shugaban kasar a zaben da ya gudana a kasar kwanan nan.

Buhari ya gana da Bakare a fadar Shugaban kasa
Buhari ya gana da Bakare a fadar Shugaban kasa
Asali: UGC

Legit.ng ta tattaro cewa malamin bai yi jawabi ga manema labarai na fadar Shugaban kasa ba bayan ganawar.

Ku tuna a baya cewa Fasto Bakare ya kasance mataimakin shugaban kasa Buhari a lokacin yakin neman zabensa a jam’iyyar Congress for Progressive Change( CPC) a zaben shugaban kasa na 2011.

KU KARANTA KUMA: Yan Igbo za su fi cin moriyar mulkin Buhari na biyu – Matasan Ohanaeze

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto na baya cewa Gwamnatin kasar Amurka ta taya shugaban kasa Muhammadu Buhari murnar sake lashe zabe.

Shugaban kasa Buhari na jam'iyyar APC ya lallasa Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP wanda ya bashi damar zarcewa akan shugabancin kasar. Sai dai Mista Abubakar da kuma jam'iyyarsa ta PDP, sun sha alwashin daukaka kara kotu kan wannan sakamakon zabe, a cewarsu babu adalci a cikinsa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel