Yan Igbo za su fi cin moriyar mulkin Buhari na biyu – Matasan Ohanaeze

Yan Igbo za su fi cin moriyar mulkin Buhari na biyu – Matasan Ohanaeze

Shugaban kungiyar matasan Ohaneze Ndigbo, Mazi Okechukwu Isiguzoro ya bayyana cewa yan Igbo za su fi kowa cin amfanin gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari a karo na biyu.

A cewar Isiguzoro, mutanen Kudu-maso gabas a wannan lokacin basu zuba kwansu a kwando guda ba domin sun zabi Buhari fiye da yanda suka yi a 2015.

Isiguzoro wanda ya tabbatar da cewa shugaban kasar zai yi wa yankin alkhairi da kuma basu gudumuwa a gwamnatinsa ya taya shugaban kasa Muhammadu Buhari murna akan nasarar da ya samu a zaben da aka guadanar kwanan nan. Kamar yanda suka bashi tabbacin goyon bayansu.

A wani jawabin da shugaban kungiyar Ohaneze Ndigbo Youth Council Worldwide, yace matasan sun yabi mutane da goyon baya da suka nuna wa Buhari.

Yan Igbo za su fi cin moriyar mulkin Buhari na biyu – Matasan Ohanaeze
Yan Igbo za su fi cin moriyar mulkin Buhari na biyu – Matasan Ohanaeze
Asali: UGC

Kungiyar tayi kira ga Ndi na jihar Imo da ta sasanta don cimma amfani ga Yan Kabilar Igbo tare da taimakawa Sanata Ben Uwajumogu na yankin Okigwe wajen samun nasara da damar zama shugaban majalisan dattijai.

KU KARANTA KUMA: Sanatoci 64, yan majalisar wakilai 151 ba za su dawo majalisa ba

A baya Legit.ng ta tattaro kungiyar Igbo mafi girma a al'adunsu, Ohanaeze Ndigbo, ta fito karara ta taya shugaban kasa murnar lashe zabe da yayi a karo na Biyu.

Sakataren kungiyar Uche Ukwukwu ne ya bayyana hakan a yayin gudanar da wani taro a Enugu a ranar Alhamis inda yace Buhari ya cancanci samun wannan nasara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel