Dr Felix: Wanda ya zo na 3 a zaben shugaban kasa ya yiwa 'yan Nigeria godiya

Dr Felix: Wanda ya zo na 3 a zaben shugaban kasa ya yiwa 'yan Nigeria godiya

- Felix Nicolas, ya godewa 'yan Nigeria, da suka bashi goyon baya a kokarinsa na zama shugaban kasar Nigeria

- Mr Felix, mai shekaru 37, shi ne dan takarar shugaban kasa mafi karancin shekaru da ya yi takara a zaben da aka gudanar ranar Asabar, 23 Fabreru, 2019

- Dan takarar shugaban kasar karkashin jam'iyyar PCP, Felix ya zo a matsayin na 3 a zaben shugaban kasa da aka kammala

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PCP, Felix Nicolas, wanda ya zo a matsayin na 3 a zaben shugaban kasa da aka kammala ranar Asabar din da ta gabata, ya godewa 'yan Nigeria, da suka bashi goyon baya a kokarinsa na zmaa shugaban kasar Nigeria.

Mr Felix, mai shekaru 37, wanda kuma shi ne dan takarar shugaban kasa mafi karancin shekaru ya yi takara a zaben shugaban kasar da aka gudanar ranar Asabar, 23 Fabreru, 2019, ya bayana jin dadinsa ne a cikin wata wasika da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis.

A cewar Nicolas, "Tarihi ba zai taba mantawa da namijin kokarin 'yan Nigeria na fitowa kwansu da kwarkwatarsu wajen kad'a kuri'unsu a babban zaben kasar da ya gudana. An kad'a kuri'u, an yi musayar yawu, a wasu wuraren, an ba hammata iska. Dukkanin wadannan abubuwan a yanzu sun wuce, su ne kuma ke nuna tabbacin dorewar Nigeria."

KARANTA WANNAN: Nasarar zabe: Manyan kasashen duniya 10 sun taya Buhari da 'yan Nigeria murna

Dr Felix: Wanda ya zo na 3 a zaben shugaban kasa ya yiwa 'yan Nigeria godiya
Dr Felix: Wanda ya zo na 3 a zaben shugaban kasa ya yiwa 'yan Nigeria godiya
Asali: UGC

A yayin da ya ke jinjinawa kokarin ofishin yakin zabensa da kuma shuwagabannin jam'iyyarsa, ya ce, "Ba zan gaza wajen yin jinjina da godiya ga dukkanin wadanda suka taimaka har zaben ya kammala. Hakika, mun samu zarafin nunawa dukkanin masu sa ido daga kasashen waje, wadanda suka cire tsammani akan tsarin zaben cewa karfin ikon komai yana hannun talakawa."

Mr Nicolas ya kara da cewa: "Ina taya sauran 'yan takarar shugaban kasa masu karancin shekaru murna akan damar da suka samu ta tsayawa takarar shugabancin kasar," yana mai cewa "Hakika wannan wani mataki ne na bunkasar demokaradiyya da kuma tunanin baiwa sabon jini damar mulkar kasar."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel