Nasarar zabe: Manyan kasashen duniya 10 sun taya Buhari da 'yan Nigeria murna

Nasarar zabe: Manyan kasashen duniya 10 sun taya Buhari da 'yan Nigeria murna

- Gwamnatocin kasashen Amurka, Saudiya, Qatar, Faransa, Burtaniya, Kenya, Afrika ta Kudu, Zimbabwe, Rasha, sun taya shugaban kasa Buhari murnar sake lashe zabe

- Shugaban kasa Buhari na jam'iyyar APC ya lallasa Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP wanda ya bashi damar zarcewa akan shugabancin kasar

- Sai dai Mr Abubakar da kuma jam'iyyarsa ta PDP, sun sha alwashin daukaka kara kotu kan wannan sakamakon zabe, a cewarsu babu adalci a cikinsa

Gwamnatin kasar Amurka ta taya shugaban kasa Muhammadu Buhari murnar sake lashe zabe. Shugaban kasa Buhari na jam'iyyar APC ya lallasa Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP wanda ya bashi damar zarcewa akan shugabancin kasar.

Sai dai Mr Abubakar da kuma jam'iyyarsa ta PDP, sun sha alwashin daukaka kara kotu kan wannan sakamakon zabe, a cewarsu babu adalci a cikinsa.

A cikin wata sanarwa daga Michael Pompeo, sakataren gwamnatin kasar Amurka, ya ce: "Amurka na taya al'ummar Nigeria murnar kammala zaben shugaban kasa lafiya, da kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa nasarar sake lashe zaben shugaban kasar."

KARANTA WANNAN: Sanatoci 64, yan majalisar wakilai 151 ba za su dawo majalisa ba

Buhari da Michael Pompeo
Buhari da Michael Pompeo
Asali: UGC

Rahotanni sun bayyana cewa, Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud na kasar Saudiya ya taya shugaban kasa Muhammadu Buhari murnar sake lashe zaben shugaban kasa. A yayin da ya ke shugaban kasa Buhari a wayar tarho a ranar Alhamis, sarki Salman ya yiwa Nigeria fatan alkairi da ci gaban arziki a mulkin Buhari karo na biyu.

Shugaban kasa Buhari ya yabawa Sarkin bisa wannan karamci da ya yi masa na kiransa a wayar tarho domin taya shi murnar lashe zaben, yana mai jaddada kudirinsa na kara karfafa dankon zumunci da alakar da ke tsakanin Nigeria da Saudiya.

Haka zalika, sarkin Qatar, Sheik Tamim bin Hamad Al Thani ya aikewa shugaban kasa sakon taya murna na sake lashe zaben shugaban kasar, yana mai yiwa shugaban kasar da 'yan Nigeria fatan ci gaban kasa da bunkasar tattalin arziki.

Shima jakan kasar Rasha a nan Nigeria, Alexey Shebarshin, ya taya Buhari murnar lashe zabe, yana mai cewa: "Ina mai farin cikin taya shugaban kasa da daukacin 'yan Nigeria murnar kammala zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya cikin kwanciyar hankali, ina fatan hakan zai daukaka darajar kasar a cikin sauran kasashen duniya."

Ministan harkokin kasashen Afrika na kasar Burtaniya, Harriett Baldwin, ya ce: "Ina taya shugaban kasa Buhari murnar yin tazarce a kujerar shugabancin Nigeria. Hakika kasar Burtaniya babbar kawa ce ga Nigeria da ma al'ummar da ke cikinta."

A wani labarin, ma'aikatar Faransa kan harkokin kasashen turai da sauran kasashe ta aike da sakon murnarta kamar haka: "Faransa na taya shugaban kasa Muhammadu Buhari murnar sake lashe zaben da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabreru. Za ta kasance mai ci gaba da tallafawa Nigeria wajen ci gaba da bunkasar tattalin arziki, samar da ayyukan yi, magance matsalolin tsaro da kuma yakar cin hanci da rashawa."

Shugaban kasa Buhari ya kuma samu sakon taya murna daga shugaban kasa Emmerson Mnangagwa na kasar Zimbabwe, da takwarorinsa, Cyril Ramaphosa na kasar Afrika ta Kudu da Uhuru Kenyatta na kasar Kenya.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel