Sanatoci 64, yan majalisar wakilai 151 ba za su dawo majalisa ba

Sanatoci 64, yan majalisar wakilai 151 ba za su dawo majalisa ba

- Zaben kasar da aka yi kwanan nan ya shafi sanatoci 64 da mambobin majalisar wakilai 151 yayinda yadda suka rasa kujerunsu

- Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki na daya daga cikin manyan da suka rasa kujerunsu domin ba zai koma majalisa ba

- A yanzu APC ce ke da mafi rinjaye a majalisar dattawa kan PDP amma har yanzu bata samu kaso biyu cikin uku na masu rinjaye ba

Yayinda APC ta kafa mafi rinjaye a majalisar dattawa, akalla sanatoci masu ci 64 da mambobin majalisar wakilai 151 ne ba za su dawo majalisar dokokin kasaar ba a raanar 9 ga watan Yuni da za a rantsar da sabbin shiga.

Sanatoci 45 kawai ne da kimanin mambobin majalisar wakilai 209 ne za su dawo majalisar tarayyar kasar.

15 daga cikin sababbin sanatocin da aka zaba sun kasance tsoffin gwamnonin jiha.

42 daga cikin sanatoci 64 da ba za su dawo ba sun rasa kujerarsu ne tun a watan Oktobar shekarar da ta gabata a zaben fidda gwanin jam’iyyunsu. Sauran 22 sun sha kaye ne a zaben majalisar dokoki da ya gudana a ranar Asabar da ya gabata.

Sanatoci 64, yan majalisar wakilai 151 ba za su dawo majalisa ba
Sanatoci 64, yan majalisar wakilai 151 ba za su dawo majalisa ba
Asali: UGC

A majalisar wakilai, adadin yan majalisa da ba za su dawo ba ya wakilci kaso 41.9% nay an majalisar 360. Ana sanya ran adadin zai karu yayinda har yanzu ba a kaddamar da sakamakon wasu mazabu ba.

Sai dai sakamako da aka saki zuwa yanzu ya nuna cewa APC ta samu sama da mambobi 200 a majlisar yayinda PDP ke da akalla sama da 100.

KU KARANTA KUMA: Allah bai kaddarci Atiku da shugabancin Najeriya ba - Inji Oshiomhole

Daga cikin manyan wadanda suka fadi zaben akwai Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki wanda ya kasance a majalisar tun 2011. Ya sha kaye a hannun Ibrahim Yahaya Oloriegbe na APC. Saraki ya kasance gwamnan jihar Kwara tsakanin 2003 da 2011.

Hazalika, wani tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio, wanda ya yi shugabanci a matsayin Shugaban marasa rinjaye kafin ya sauya sheka zuwa APC a watan Agusta da ya gabata, ma ya rasa kujerarsa. Akpabio ya kasance gwamnan Akwa Ibom tsakanin 2007 da 2015.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel