Da dumi-dumi: Amurka tana neman dan Osama bin Laden ruwa a jallo

Da dumi-dumi: Amurka tana neman dan Osama bin Laden ruwa a jallo

- Kasar Amurka tana neman dan tsohon shugaban kungiyar Al-Qaeda Osama bin Laden, Hamza bin Laden ruwa a jallo

- An yi alkawarin bayar da tukwucin kudin Dala Miliyan Daya ga duk wanda zai iya bayar da bayani a kansa

- Ana hasahen cewa Hamza bin Laden ya fara karfi a matsayin jagora na kungiyoyin ta'addanci a kasashen laraba

Da dumi-dumi: Amurka tana neman dan Osama bin Laden ruwa a jallo
Da dumi-dumi: Amurka tana neman dan Osama bin Laden ruwa a jallo
Asali: Twitter

A jiya Alhamis ne kasar Amurka ta yi alkawarin bayar da tukwuicin dala miliyan daya ga duk wanda ya bayar da bayani a kan inda za a gano dan tsohon shugaban kungiyar Al-Qaeda Osama bin Laden duba da cewa ya gaji mahaifinsa a matsayin jagoran kungiyar ta'adanci.

DUBA WANNAN: Yadda Buhari ya yi murdiyya wajen lashe zaben 2019 - Sheikh Ahmad Gumi

Channels TV ta ruwaito cewar a halin yanzu ba a san takamamen inda Hamza bin Laden wadda ake yiwa lakabi da 'Yariman Jihadi' ya ke ba.

A shekarun da suka gabata, an rika samun rahotanni da ke hasashen cewar yana kasar Pakistan ko Afganistan ko kuma yana tsare a wani gida a kasar Iran.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel