Kaico! An kashe na’ibin limamin Masallaci a yayin murnar nasarar Buhari

Kaico! An kashe na’ibin limamin Masallaci a yayin murnar nasarar Buhari

A yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari da iyalansa suke can fadar gwamnati Aso Rock Villa suna jin dadin rayuwa hankalinsu a kwance, su kuwa wasu mutanen kashe kansu suke yi tare da kashe wasu da sunan wai murnar samun nasarar Buhari a zabe.

Wasu kuma ko basu mutu a sakamakon haka ba, amma sun jikkata, kuma sun jikkata wasu, ko kuma akalla sun jefa rayuwarsu cikin hatsari tare da kasancewa barazana ga rayuwar wasu, duk a cikin murnar Buhari, a iya kiran wadannan sun fi mai kora shafawa.

KU KARANTA: Minista ya kaddamar da wani katafaren aiki a garin Buhari kwanaki kadan bayan yaci zabe

Anan ma wani na’ibin Limami ne a jahar Adamawa ya rasa ransa sakamakon irin wannan mummunan halayya ta wasa da ababen hawa da wasu jama’a suka nuna wai da sunan suna murnar samun nasarar da Buhari ya samu a zaben shugaban kasa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a garin Mubi, a lokacin hatsari ya rutsa da Malam Adamu, dattijon arziki kuma na’ibin limami a masallacin rukunin gidaje na Shuwarin, yayin da yake kokarin tsallaka titi a ranar Talata.

A lokacin da Malam Adamu ya nemi ya tsallaka titi ne sai wani direban Keke Napep dake tukin ganganci ya tsoratashi, wanda hakan yasa ya koma baya, koma bayan da yayi keda wuya sai kwatsam wani Keke Napep ya daukeshi.

Sai dai shaidun gani da ido sun tabbatar da cewar direban Keke Napep din daya buge Malam baya cikin masu tukin ganganci da sunan murnar Buhari, asali ma kokari yake ya kauce ma taho mu gama da direbobin dake gangancin.

Har sai a washegari ranar Laraba ne Malam Adamu ya rasu, kuma aka gudanar da jana’izarsa a ranar kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar, shima dattijon daya kadeshi bisa tsautsayi ya samu halartar jana’izar tasa.

A wani labarin kuma, wani jami’in rundunar Sojan Najeriya ya kusa halaka wasu magoya bayan shugaban Buhari alokacin daya bude musu wuta yayin da suke murnar samun nasarar da yayi a zaben daya gabata a garin Numan na jahar Adamawa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel