Ku shigo cikin al’amuran zaben gwamnoni – Tambuwal ya gayyaci kasar Amurka

Ku shigo cikin al’amuran zaben gwamnoni – Tambuwal ya gayyaci kasar Amurka

Gwamnan jahar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya yi kira ga gwamnatin kasar Amurka da ta taimaka ta shigo cikin al’amuran zaben gwamnoni da hukumar zabe mai zaman kanta zata gudanar a ranar Asabar, 9 ga watan Maris.

Tambuwal yayi wannan kira ne a ranar Alhamis, lokacin da jakadan kasar Amurka, Stuart Symington ya kai masa ziyara a ofishinsa dake fadar gwamnatin jahar Sakkwato a garin Sakkwato, inda ya bayyana damuwarsa da yadda zake cin zarafin yan adawa a siyasar Najeriya.

KU KARANTA: Minista ya kaddamar da wani katafaren aiki a garin Buhari kwanaki kadan bayan yaci zabe

A jawabinsa, Tambuwal ya bayyana ma jakadan cewa sun ga yadda aka ci zarafin tare da kama shuwagabanni da magoya bayan babbar jam’iyyar adawa ta PDP, inda yace ko kadan bai dace ba, don suke neman taimakon kasar Amurka game da hakan.

Majiyar Legit.ng ta ruwaitoshi yana cewa: “Kiran da mukeyi shine kada a musguna ma jama’a masu zabe, ko kuma a yi musu barazana, saboda an tsoratar da magoya bayanmu a zaben daya gabata har ta kai ga sun yanke shawarar kin yin zabe a zabe mai zuwa na ranar 9 ga watan Maris.

“Da wannan nake kira a jakadan kasar Amurka daya ja hankalin gwamnatin Najeriya su kyale al’umman Najeriya su zabi wanda suke so a zaben gwamnoni da na yan majalisun jihohi. Wasu sun sun je suna ta kona gidajen mutanen da ake ganin suna adawa da gwamnati a garin nan.” Inji shi.

Daga karshe ya gode ma jakadan bisa wannan ziyara daya kai masa, inda ya bayyana hakan a matsayin muhimmin lamari ga cigaban zaman lafiya da dimukradiyya a jahar. Shima a nasa jawabin, jakadan ya yaba da kyakkyawar tarbar daya samu.

Inda yace ya je Sakkwato ne don ya karfafa bukatar samun ingantaccen yanayin zaman lafiya da lumana a yayin lokuttan gudanar da zaben 2019, domin a cewarsa babu wani cigaba da za’a samu idan babu zaman lafiya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel