Karkatar da kudin makamai: Tsohon Sojan Saman Najeriya zai yi shekaru 7 a kurkuku

Karkatar da kudin makamai: Tsohon Sojan Saman Najeriya zai yi shekaru 7 a kurkuku

- Kotu ta yankewa wani tsohon Sojan Saman Najeriya hukuncin zaman gidan yari ne shekaru 7 bayan an same shi da laifin karkatar da kudin makamai

- Tsohon sojan, Air Vice Marshal Tony Omeniyi ya karkatar da zunzurutun kudi Naira Milyan 136 na sayan makamai ne a shekarar 2014

- Hukumar EFCC tayi nasarar kwato Naira Miliyan 62 daga hannunsa kuma kotu ta bayar da umurnin a mayar da kudin baitil malin gwamnati

Karkatar da kudin makamai: Tsohon Sojan Saman Najeriya zai yi shekaru 7 a kurkuku
Karkatar da kudin makamai: Tsohon Sojan Saman Najeriya zai yi shekaru 7 a kurkuku
Asali: Twitter

Wata babban kotun tarayya ta zartas da hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru bakwai a kan wani tsohon Sojan saman Najeriya, Air Vice Marshal Tony Omeniyi bisa samunsa da laifin karkatar da zunzurutun kudi Naira Milyan 136 na sayan makamai domin amfanin sojojin saman Najeriya a yayin da ya ke aiki.

DUBA WANNAN: Kin amincewa da sakamakon zabe: Abubuwa 6 da Atiku ya fadi a jawabinsa

Wanda aka yanke wa hukuncin, ya karbi cin hanci ne daga SkyExperts Nigeria Limited, a 2014 a lokacin yana shugaban wani kamfani da ke karkashin rundunar sojojin sama na Najeriya mai suna Aeronautical Engineering and Technical Services Limited.

Bayan kotu ta tabbtar da laifuka uku da ake tuhumarsa da aikawatawa, Alkalin kotun, Justice Nnamdi Dimgba ya yanke masa shekaru bakwai a kan kowanne laifukan sai dai ya ce za a hade masa shekarun zaman gidan yarin.

Alkalin ya bayar da umurnin gwamnati ta karbe kamfanin Huzee Nigeria Limited da akayi amfani da ita wurin karbar kudin rashawar Naira Miliyan 136 daga SkyExperts Nigeria Limited.

Kotun kuma ta bayar da umurnin a mika Naira Miliyan 62 da Hukumar Yaki da Rashawa EFCC ta kwato daga Omeniyi zuwa ga baitul malin gwamnatin tarayya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel