Dan takarar gwamna ya kori 'yan gudun hijirar da ya taimaka don sun zabi Buhari

Dan takarar gwamna ya kori 'yan gudun hijirar da ya taimaka don sun zabi Buhari

Dan takarar gwamna a karkashin tutar jam'iyar APGA a jihar Zamfara, Alhaji Sani Abdullahi Shinkafi, a jiya Laraba ya tabbatar da korar dukkan "yan gudun hijirar da ya sauke a gidajen sa dake garin Shinkafi saboda sun zabe shugaba Buhari a Zaben ranar Assabar da ta gabata.

Alhaji Sani Shinkafi ya tabbatar da hakan ne a wani taron manema labarai da gamayyar jam'iyun adawa daga jihar ta Zamfara suka kira a garin Gusau a jiya Laraba 27 ga watan Fabrariru 2019 inda suke kalubalantar zaben da ya gudana a jihar.

Dan takarar gwamna ya kori 'yan gudun hijirar da ya taimaka don sun zabi Buhari
Dan takarar gwamna ya kori 'yan gudun hijirar da ya taimaka don sun zabi Buhari
Asali: UGC

KU KARANTA: Kawo karshen rikicin Zamfara ba yanzu ba - Gwamna Yari

Yace "Na umurci dukkan "yan gudun hijira dake zaune a cikin gidaje na dake garin Shinkafi da su gaggauta fita daga gidajen saboda basu da kyakkawan tunani a rayuwar su (basu da hankali)". Ya cigaba da cewa "Mutanen da suka zaba sune mutanen da sukayi sanadiyar barin gidajen "yan gudun hijrar saboda rashin samar masu ingantaccen tsaro, da kuma abubuwan more rayuwa, amma suka sake zabar su" inji shi.

Yace tun a farko sai da yaja kunnen su akan kada su sake zabar su saboda halin da suka saka su, amma sai da suka zaba. Ya zargi "yan gudun hijrar da zabar cigaba da rayuwa cikin kaskanci ta hanyar sayar da "yancin su a lokacin zabe ga miyagun mutane".

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel