Rigimar rijiyar man fetur: Mohammed Abacha ya shigar da karar FG a kotun daukaka kara

Rigimar rijiyar man fetur: Mohammed Abacha ya shigar da karar FG a kotun daukaka kara

Muhammad Abacha, babban dan tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soji, Marigayi Janar Sani Abacha, ya shigar da karar gwamnatin tarayya, kamfanin hakar man fetur na Shell, da karin wasu a gaban kotun daukaka kara a kan rigimar rijiyar man fetur mai lamba OPL 245 ta kamfanin Malabu.

A takardar shigar da karar, Muhammad ya bukaci kotun daukaka karar ta tilasta wata babbar kotun gwamnatin tarayya sauraron uzurin su a kan kalubalantar da su ke yi wa gwamnatin tarayya da kamfanin Shell.

A kara ta farko da su ka shigar, Muhammad da kamfanin ‘Pecos Energy’ na kalubalantar gwamnatin tarayya da karkatar da hannun jarin da su ke da shi a rijiyar man fetur mai lamba OPL 245.

Rigimar rijiyar man fetur: Mohammed Abacha ya shigar da karar FG a kotun daukaka kara
Muhammad Abacha
Asali: Getty Images

Yanzu haka Muhammad na neman kotun daukaka karar ta tilasta kotun gwamnatin tarayya bashi damar yin gyara domin ya cire gwamnatin tarayya da kuma ministan man fetur daga cikin wadanda ya ke kara, bukatar da kotun ta ki amincewa da ita bayan wadanda ake kara sun nuna rashin amincewar su da hakan.

DUBA WANNAN: Shugaban kungiyar kwadago ya yi murabus bayan samun mukami a gwamnati

Ya yanzu dai kotun ba ta sa wata rana domin fara sauraron karar da Mohammed ya shigar ba.

Muhammad na daga cikin ‘yan takarar neman kujerar gwamnan jihar Kano a zaben gwamnoni da mambobin majalisar dokokin jihohi da za a yi ranar 9 ga watan Maris.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel