Nasarar Buhari: Kwamitin sulhun Abdulsalam ya gana da Atiku da Obi

Nasarar Buhari: Kwamitin sulhun Abdulsalam ya gana da Atiku da Obi

Yanzu haka mambobin kwamitin sulhu da sasanto na can su na gana wa da dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, da shugaba Buhari ya kayar a zaben shugaban kasa da aka yi ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu.

Kwamitin da tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soji, Abdulsalami Abubakar, ke jagoranta na ganawa da Atiku, dan takarar mataimakin shugaban kasa, Peter Obi, da manyan jagororin kwamitin yakin neman zaben sa.

Ragowar mambobin kwamitin da Abdulsalami ke jagoranta sun hada da Matthew Kuka, Kadinal John Onaiyekan, da Rabaran Atta Barkindo.

Legit.ng ta fahimci cewar ganawar ba za ta rasa nasaba da ikirarin Atiku na kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa a kotu ba.

Akwai shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Uche Secondus, shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, da wasu manya da ke da kusanci da Atiku a wurin ganawar.

Da duku-dukun safiyar ranar Laraba, 27 ga watan Fabarairu, ne INEC ta bayyana cewar shugaba Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC ne ya lashe zaben kujerar shugaban kasa.

Nasarar Buhari: Kwamitin sulhun Abdulsalam ya gana da Atiku da Obi
Nasarar Buhari: Kwamitin sulhun Abdulsalam ya gana da Atiku da Obi
Asali: Twitter

Da ya ke sanar da sakamakon zaben, Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban INEC, y ace Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 15,191,847 da su ka bashi nasara a kan abokin hamayyar sa, Atiku Abubakar, na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 11,255,978.

A wani jawabi da ya fitar bayan shugaban INEC ya bayyana sakamako, Atiku y ace akwai alamun tambaya a kan sakamakon zaben tare da ikirarin cewar zai kalubalance shi a kotu.

DUBA WANNAN: Shugaban kungiyar kwadago ya yi murabus bayan samun mukami a gwamnati

A wani taro da ya yi da manema labarai na duniya a Abuja, Atiku ya bayyana sakamakon zaben da cewar ‘fashi’ ne ga zabin ‘yan Najeriya.

A cewar sa, alkaluman da INEC ta bayyana a sakamakon zaben ba daidai ba ne.

Atiku ya ce: “mu na da alkaluman sakamakon zabe na gaskiya, mu na kuma da bayanai a kan yadda aka gudanar da zaben ranar 23 ga watan Fabrairu.

“Ba wai ina magana ne a matsayin dan jam’iyyar PDP ba. Ina Magana ne a matsayin dan Najeriya da gwamnatin Buhari ta yi wa fashin nasara a zaben da aka yi ranar Asabar. Sakamakon da aka bayyana ba shine abinda ‘yan Najeriya su ka zaba ba.

“A saboda wannan dalili ne ni, Atiku Abubakar, na ki amincewa da sakamakon da INEC ta bayyana a kan cewar Muhammadu Buhari ne ya lashe zabe ta hanyar samun haramtattun kuri’u ma fi rinjaye,” a kalaman Atiku.

Atiku ya kara da cewa a tsawon shekaru fiye da 30 da ya yi ya na siyasa bait aba ganin lalataccen zabe irin wanda INEC ta gudanar ranar Asabar da ta gabata ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel