Yan Najeriya 30,000 sun dawo garin da Boko Haram suka kai farmaki

Yan Najeriya 30,000 sun dawo garin da Boko Haram suka kai farmaki

Akalla yan Najeriya 30,000 ne suka dawo kasar tun ranar Talata, 26 ga watan Fabrairu daga kasar Kamaru.

Yan gudun hijiran sun dawo ne bayan sun bar mahaifarsu ta Rann, wanda ya fuskanci hare-haren mayakan Boko Haram a wannan shekarar, hukumar bayar da akaji ta UN ta bayyana hakan a ranar Alhamis, 28 ga watan Fabrairu.

Yan Najeriya 30,000 sun dawo garin da Boko Haram suka kai farmaki
Yan Najeriya 30,000 sun dawo garin da Boko Haram suka kai farmaki
Asali: Depositphotos

Sun dawo kasar ne bayan jami’an Najeriya sun ziyarce su sannan suka karfafa masu gwiwar dawowa kasar bayan sun basu tabbacin cewa za a inganta harkar tsaro a yankin, cewa , UNHCR.

Hukumomin kasar Kamaru ma sun ba jami’an UNHCR tabbacin cewa ba za a tursasawa yan gudun hijira komawa kasar ba, Reuters ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Matar Tinubu na shirin zama mataimakiyar Shugaban Majalisar Dattawa

A wani lamari na daban, mun ji cewa wata Baiwar Allah mai suna Tope Ogba ta bada labarin yadda Mijin ta mai suna Gabriel Ogba ya ke yi wa ‘Ya ‘yan da su ka haifa fyade. Tope Ogba ta fadawa kotu wannan mugun labari ne a Garin Legas.

Wannan mata take cewa Mijin ta na aure, yana neman Yaran su ‘yan mata masu shekaru 20 da kuma mai shekara 25 a Duniya. Baiwar Allah tace lamarin mai gidan na ta bai tsaya nan ba inda ta kai yana neman karamar kanwar su.

A farkon makon nan Tope Ogba ta sanar da wani kotu mai karbar laifuffuka na musamman da ke cikin Garin Ikeja a jihar Legas yadda Mai gidan na ta yake yi wa yarinyar su ‘yar auta da ba ta wuce shekaru 13 da haihuwa a Duniya ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel