‘Yan takarar gwamna 2 sun jaye wa PDP don a kayar da El-Rufa’i a Kaduna

‘Yan takarar gwamna 2 sun jaye wa PDP don a kayar da El-Rufa’i a Kaduna

Dan takarar neman zama gwamnan jihar Kaduna a karkashin inuwar jam’iyyar APGA, Dakta Polycaro Gankon, da takwaran san a jam’iyyar LM, Kwamred Ezekiel Habila, sun janye wad an takarar jam’iyyar PDP, Isa Ashiru Kudan.

Da ya ke magana da manema labarai amadadin takwaran san a jam’iyyar LM da su ke tare a gaban dandazon magoya bayan su, Dakta Gankon y ace sun yanke shawarar janye wa ne bayan tuntubar ‘yan jam’iyya da ‘yan uwa da abokai domin su hada karfi wuri guda domin ceto jihar Kaduna daga dumbin kalubale da ta ke fuskanta.

Ya kara da cewa bas u fuskanci matsin lamba a kan su janye takarar su kuma ba su janye saboda an ba su kudi ba. “Mun yanke wannan shawara ne don kishin jihar Kaduna, kuma mu na kira ga dukkan magoya bayan mu da su mara wa jam’iyyar PDP baya a zaben gwamna domin ta kawo ma na cigaba.

“Mu na kira ga magoya bayan mu da kada su bari sakamakon zaben shugaban kasa da aka yi magudi ya karya ma su guiwa, dole mu tashi tsaye wajen ganin mu yi tururuwa wajen fita mu zabi jam’iyyar PDP.

‘Yan takarar gwamna 2 sun jaye wa PDP don a kayar da El-Rufa’i a Kaduna
Malam Nasir El-Rufa’i
Asali: Depositphotos

“Mu na da ragowar ‘yan takara a matakin majalisar jiha, ba su janye ba, a saboda haka mu na so ku zabe su amma ku zabi PDP a matakin gwamna.

DUBA WANNAN: Ali Nuhu da jerin fitattun jarumai da su ka taya Buhari murna

Da ya ke karin bayani, dan takarar jam’iyyar LM, Kwamred Habila, ya ce, “a ra’ayin mu da na ‘yan jam’iyyun mu da magoya bayan mu, wannan mataki da mu ka dauka shine ya fi dacewa saboda matukar mu na son kawo cigaba a jihar mu ta Kaduna, dole mu hada karfin wuri guda domin dakile irin magudin da aka yi ma na a Kaduna lokacin zaben shugaban kasa."

‘Yan takarar biyu sun ce za su yi amfani da albarkatun su na dukiya da jama’a domin ganin dan takarar jam’iyyar PDP ya kai ga nasara tare da yin kira ga duk ma su kaunar jihar Kaduna su yi koyi da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel