Tonon-silili: An gano wani gwamnan APC da bai zabi Buhari ba a zaben shugaban kasa

Tonon-silili: An gano wani gwamnan APC da bai zabi Buhari ba a zaben shugaban kasa

Yayin 'ya'yan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ke cigaba da gudanar bukukuwan murnar su ta nasarar da suka samu na zarcewar shugaba Buhari a karo na biyu bayan ya kada abokin hamayyar sa, Atiku Abubakar, an kuma bankado wata sabuwar badakala.

Kamar yadda muka samu, wani bangare na jam'iyyar ta All Progressives Congress (APC) a jihar Ondo dake a shiyyar Kudu maso yammacin kasar nan karkashin kungiyar APC Mandate Group ta ce gwanan jihar bai zabi shugaba Buhari ba a zaben da aka gudanar ranar Asabar.

Tonon-silili: An gano wani gwamnan APC da bai zabi Buhari ba a zaben shugaban kasa
Tonon-silili: An gano wani gwamnan APC da bai zabi Buhari ba a zaben shugaban kasa
Asali: UGC

KU KARANTA: Dalilan Atiku 5 na kin amincewa da zaben 2019

Kungiyar wadda ta bayyana hakan a cikin wata sanarwar manema labarai dauke da sa hannun kakakin ta Kwamared Olugbenga Bojuwomi ta kuma ce suna kira da jam'iyyar a mataki na kasa ta rushe dukkan shugabannin jam'iyyar ta APC a jihar.

Haka ma dai kungiyar ta ce faduwar da jam'iyyar tayi a jihar zaben shugaba Buhari bai zo mata da mamaki ba domin kuwa ta fada cewa gwamnan daman baya tare da shugaba Buhari kuma yana yiwa jam'iyyar zagon kasa ne kawai.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa jihar Ondo tana daya daga cikin jahohin da dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya lashe a zaben da aka gudanar ranar Asabar din da ta gabata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel