Yanzu Yanzu: Matar Tinubu na shirin zama mataimakiyar Shugaban Majalisar Dattawa

Yanzu Yanzu: Matar Tinubu na shirin zama mataimakiyar Shugaban Majalisar Dattawa

Bayan lashe zabe a karo na uku, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayyana muradin ta na zama mataimakiyar shugaban majalisan dattawa.

Ta bayyana hakan ne a hira da tayi da manema labarai a gidan ta.

Ta ce: “Mun yi gwamna a baya. A lokacin da mijina yayi gwamna, na kasance uwargidan gwamnan jihar Lagas, wannan ya kasance karo na uku da nake a matsayin sanata.

“Wanene yace ba zan iya sha’awan zama shugaban Majalisan dattawa ba? Bana son zama shugaban majalisa amman na dade ina sha’awan zama mataimakiyar shugaban majalisa saboda ina da ayyuka da dama da nake son in gudanar.”

Yanzu Yanzu: Matar Tinubu na shirin zama mataimakiyar Shugaban Majalisar Dattawa
Yanzu Yanzu: Matar Tinubu na shirin zama mataimakiyar Shugaban Majalisar Dattawa
Asali: UGC

Ta kara da cewa, a matsayina na mace, “ya kamata in dunga kamanta wa rayuwa na. Wannan nuni ne cewa mace zata iya kasancewa da aiki duk da cewa tana da aure, yankina na bukatan ayyuka masu nauyi. Wannan ne yasa ban gabatar da kudurori da yawa ba.”

A wani lamari na daban, mun ji cewa Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Adams Oshiomhole ya ce kaddara bai nufi tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da mulkin Najeriya ba.

Ya fadi haka ne a taron manema labarai yayinda yake mayar da martani akan rashin amincewa da sakamakon zabe da dan takaran jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya nuna.

KU KARANTA KUMA: Matashiyar da ta shiga jami’a a shekara 15 sannan ta kammala a shakara 18 ta sanarda labarinta

Oshiomhole yace koarin Atiku na son ganin ya zama shugaban kasa har karo na hudu ya tarwatse a zaben shugaban kasa a lokacin da shugaban kasa mai ci, Muhammadu Buhari ya lashe zaben.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel