Ruwa-a-jallo: Rudani yayin da wani malamin addinin da ke tada matattu ya yi batan dabo

Ruwa-a-jallo: Rudani yayin da wani malamin addinin da ke tada matattu ya yi batan dabo

Yanzu haka dai ana cikin rudani ne a wani gari dake kasar Afrika ta kudu biyo bayan batan dabon da wani babban malamin addinin kirista kuma shugaban majami'un Alleluia watau Fasto Alph Lukau da yace yana tada matattu.

Sai dai yayin da mutane ke tururuwa zuwa majami'ar ta Alleluia, an nemi Faston sama ko kasa an rasa sai ma dai karin tarin yawan jami'an tsaro da suka tsaurara matakan tsaron su a majami'ar ta hanyar hana shiga sai wasu 'yan tsiraru kawai.

Ruwa-a-jallo: Rudani yayin da wani malamin addinin da ke tada matattu ya yi batan dabo
Ruwa-a-jallo: Rudani yayin da wani malamin addinin da ke tada matattu ya yi batan dabo
Asali: UGC

KU KARANTA: Buba Galadima ya bayyana bayan kwanaki

Legit.ng Hausa ta samu cewa shi dai babban malamin ya fara yin suna ne bayan da labarin ya tada wani matacce ya soma yawo kamar wutar jeji a garin wanda hakan ya sa mutane yin fitar farin dango don zuwa gane ma idon su.

Sai dai kuma daga baya sai wasu labarai na laifin damfara da kuma zamba cikin aminci da wasu mutane da dama suka bada labarin babban malamin yayi masu a baya wanda hakan ya fara jefa shakku a zukatan al'umma mabiyan sa.

Wasu labaran ma dake fitowa akan malamin na nuni ne da cewa akwai kararraki da dama a gaban kotuna da aka shigar da shi malamin saboda zargin munanan halaye.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel