Da duminsa: Yadda 'yan APC suka amshe dalolin Atiku suka zabi Buhari - Oshiomhole

Da duminsa: Yadda 'yan APC suka amshe dalolin Atiku suka zabi Buhari - Oshiomhole

Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Adams Oshiomhole ya bayyana yadda 'yan jam'iyyar suka karbe daloli daga hannun dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP gabanin zaben 2015.

Amma daga baya kuma suka mika tikitin takarar ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Oshiomhole ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a jawabin da ya yiwa duniya a Abuja bayan Atiku ya yi nashi jawabin a ranar Laraba inda Atiku ya yi ikirarin cewa zaben da aka gudanar a ranar Asabar itace mafi muni a tarihin Najeriya.

Oshiomhole ya bayyana yadda 'yan APC suka amshe dalolin Atiku kuma suka zabi Buhari
Oshiomhole ya bayyana yadda 'yan APC suka amshe dalolin Atiku kuma suka zabi Buhari
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yadda Buhari ya yi murdiyya wajen lashe zaben 2019 - Sheikh Ahmad Gumi

Bayan ya soki Atiku bisa yadda ya rika sauya jam'iyyun siyasa tun bayan saukansa daga mulki a matsayin mataimakin shugaban kasa a 2007, Oshiomhole ya bayyana yadda Atiku ya bawa 'yan jam'iyyar APC cin hanci gabanin zaben fidda gwani na APC:

"Ya samu mu a Legas, ya raba mana daloli, shi kuma Shugaba Muhammadu Buhari ya shaidawa da ni cewa bashi da daloli da zai bamu, Bani da kamfanin Intel; Bani da asusun ajiya a kasashen waje kuma ko da ina dashi ba zan bayar ba. Ni zuciya ta kawai zan bayar.

"Wasu daga cikin 'yan jam'iyyar APC sun karbi daloli daga hannun Atiku kuma duk da haka zuka zabi Buhari a matsayin dan takarar shugaban kasar mu."

Ku biyo mu domin karin bayani ...

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel