Yadda aka yiwa Akpabio magudin zabe a jihar Akwa Ibom - Oshiomhole

Yadda aka yiwa Akpabio magudin zabe a jihar Akwa Ibom - Oshiomhole

- Shugaban jam'iyyar APC Adams Oshiomhole ya yi ikirarin cewa magudi aka yi a zaben sanata na jihar Akwa Ibom shi yasa sanata Godswill Akpabio ya sha kaye

- Oshiomhole ya ce jam'iyyar APC tuni ta shigar da korafi ga Hukumar Zabe INEC domin magudin da ya yi ikirarin an tafka a zaben

- A baya dai, Adams Oshiomhole ya yi ikirarin cewa hukumar INEC tana yiwa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) aiki

Dalilin da yasa Akpabio ya sha kaye a zabe - Oshiomhole
Dalilin da yasa Akpabio ya sha kaye a zabe - Oshiomhole
Asali: Twitter

Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC), na kasa Kwamared Adams Oshiomhole ya yi ikirarin cewa an yiwa Sanata Godswill Akpabio magudi ne a zaben sanata a jihar Akwa Ibom shi yasa ya.

Akpabio da ya yi takara a karkashin jam'iyyar APC dai ya rasa kujerarsa ta sanata ne ga Christopher Ekpenyong na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 'yan majalisun tarayya da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata.

DUBA WANNAN: Kin amincewa da sakamakon zabe: INEC ta mayarwa PDP martani

Oshiomhole ya yi wannan jawabin ne a sakatariyar jam'iyyar APC da ke Abuja a ranar Alhamis.

Ya ce abin mamaki ne yadda jam'iyyar PDP ke korafi a kan sakamakon zabe a jihar Akwa Ibom duk da cewa su sukayi nasara.

"Mun rubuta korafi zuwa ga INEC a kan yadda aka yi mana magudi a jihar Akwa Ibom sai dai wani abin mamaki shine PDP na korafi a kan zaben Akwa Ibom duk da cewa su suka lashe zaben," inji shi.

"Ta yaya za ayi INEC za ta soke zabukka a rumfunnan zabe da yawa a jihar Akwa Ibom da wasu jihohi da yawa kuma duk da hakan aka sanar cewa 'yan takarar jam'iyyar PDP ne su kayi nasara. Haka aka yiwa Sanata Akpabio magudi a jihar Akwa Ibom," inji shi.

A baya, Oshiomhole ya yi ikirarin cewa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC tana yiwa jam'iyyar PDP aiki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel