Allah bai kaddarci Atiku da shugabancin Najeriya ba - Inji Oshiomhole

Allah bai kaddarci Atiku da shugabancin Najeriya ba - Inji Oshiomhole

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Adams Oshiomhole ya ce kaddara bai nufi tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da mulkin Najeriya ba.

Ya fadi haka ne a taron manema labarai yayinda yake mayar da martani akan rashin amincewa da sakamakon zabe da dan takaran jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya nuna.

Allah bai kaddarci Atiku da shugabancin Najeriya ba - Inji Oshiomhole
Allah bai kaddarci Atiku da shugabancin Najeriya ba - Inji Oshiomhole
Asali: Twitter

“Girman kai ne ganin an alakanta mu da shugabantar shi nan gaba.

“Kaddara baza ta taba ba Atiku damar zama shugaban kasar Najeriya ba,” a cewar Mista Oshiomhole.

“Shugabanci ba komai bane illa kyawun hali.

KU KARANTA KUMA: Kalli yadda Aisha Buhari ta taka rawa bayan mijinta ya lashe zabe (bidiyo)

“Maitan son mulki irin na Atiku a bayyane yake, har ya kai ga yin rikici da ubangidan shi, tsohonshugaban kasa Olusegun Obasanjo, da kada yayi tsaya takara karo na biyu.”

Oshiomhole ya kuma jadadda cewa yunkurin Atiku don ganin ya zama shugaban kasa har karo na hudu ya tarwatse a zaben shugaban kasa a lokacin da shugaban kasa mai ci, Muhammadu Buhari ya lashe zaben.

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa kungiyar Igbo mafi girma a al'adunsu, Ohanaeze Ndigbo, ta fito karara ta taya shugaban kasa murnar lashe zabe da yayi a karo na Biyu.

Sakataren kungiyar Uche Ukwukwu ne ya bayyana hakan a yayin gudanar da wani taro a Enugu a ranar Alhamis inda yace Buhari ya cancanci samun wannan nasara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel