Yanzu-yanzu: Da yiwuwan Buhari ya sallami dukkan ministocinsa - Fadar shugaban kasa

Yanzu-yanzu: Da yiwuwan Buhari ya sallami dukkan ministocinsa - Fadar shugaban kasa

Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban kasa, ya bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari zai sallami zai sallami ministocinsa kafin ranan 29 ga watan Mayu.

Bayan hawa mulki a shekarar 2015, sai da ya kwashe watanni shida kafin nada ministoci kuma hakan ya jawo masa cece-kuce.

Ya yi bayani a tashar Arise TV, Femi Adesina ya ce shugaban kasa ba zai dau lokaci irin haka kafin ya nada ministoci ba wannan karon.

Yayinda kae tambayesa shin shugaba Buhari zai sallami ministocinsa, Adesina yace : "Wani abu daya da mulki shine wa'adinka na farko shekara hudu ne."

"Wa'adinsa zai kare ranar 29 ga watan Mayu, kuma gab da ranan, da yuwuwan shugaban kasa zai sallami dukkan wadanda ya nada. Haka ake ko da yaushe."

"Shugaban zai godewa wadanda sukayi masa aiki sannan ya sallamesu. Idan aka rantsar da shi a wa'adi na biyu, sai ya saka wasu nade-nade, zai nada hadimansa, zai nada ministoci."

KU KARANTA: Hukumar INEC na cikin ganawa don sake duba zaben shugaban kasa

Shugaba Buhari ya samu nasara a zaben da hukumar INEC ta gudanar ranar Asabar, 23 ga watan Febrairu, 2019.

Buhari na jam'iyyar APC ya yi nasara ne da bayan samun kuri'u miliyan 15 domin lallasa Atiku Abubakar na PDP wada ya samu kuri'u miliyan 11.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel