Dan takarar APC a Kwara ya fadi matakin da zai dauka a kan Saraki da tsaffin gwamnoni

Dan takarar APC a Kwara ya fadi matakin da zai dauka a kan Saraki da tsaffin gwamnoni

Dan takarar gwamna na jam'iyyar All Progressives Congress, APC a jihar Kwara, Alhaji AbdulRahman AbdulRazaq ya ce zai soke dokar da ta halastawa tsaffin gwamnoni da mataimakansu fansho domin samun kadaden da za a yiwa al'umma aiki idan ya yi nasarar lashe zabe.

Ya yi kira ga al'umma su zabe shi da ma sauran dukkan 'yan takarar jam'iyyar APC a zaben 'yan majalisun jiha da za a gudanar a ranar 9 ga watan Maris a Kwara.

Abdulrazak ya yi wannan jawabin ne a wurin kamfen da aka gudanar a Omu Aran da ke Kwara ta Kudu da kuma garin Pategi da ke Kwara ta Arewa.

DUBA WANNAN: Kin amincewa da sakamakon zabe: Abubuwa 6 da Atiku ya fadi a jawabinsa

Dan takarar APC a kwara ya fadi matakin da zai dauka a kan Saraki
Dan takarar APC a kwara ya fadi matakin da zai dauka a kan Saraki
Asali: Depositphotos

Ya ce, "Ya kamata mu canja wasu dokoki marasa kyau. Za mu soke wannan dokar ta fansho idan an zabe mu.

"Alfarma ce mutum ya zama gwamnan jiha amma zalunci ne a ce duk wanda ya zama gwamna zai rika karbar fansho fiye da mutanen da suka kwashe dukkan rayuwarsu suna yiwa jiharsu aiki. Ba zamu amince da haka ba amma muna bukatar 'yan majalisu da yawa domin sauya wannan dokar ta zalunci."

Ma'aikata da al'ummar jihar Kwara sun dade suna korafi a kan dokar fansho din na tsaffin gwamnoni da mataimakin gwamnoni inda suke ganin zalunci ne da rashin adalci tare da wawure kudin jihar.

Abdulrazaq ya ce gwamnatinsa za ta mayar da hankali wurin inganta tsaro, habbaka tattalin arziki da tallafawa matasa domin kawar da zaman kashe wando da kawar da 'yan daba da sauran bata gari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel