Kin amincewa da sakamakon zabe: Muna jiran Atiku a kotu - Oshimohole

Kin amincewa da sakamakon zabe: Muna jiran Atiku a kotu - Oshimohole

Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress, APC na kasa, Adams Oshiomhole ya ce jam'iyyar ta na shirin gamuwa da dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party, Atiku Abubakar a kotu.

Atiku ya bayyana cewa bai taba ganin zabe da ya fi wannan muni ba a cikin shekaru 30 da suka gabata kuma ya dau alwashin garzayawa kotu domin a bi masa hakkin sa.

Sai dai shugaban na APC ya ce tun da fari Atiku ya ayyana a ransa cewa idan dai ba shine ya yi nasara ba toh sahihiyar zabe aka gudanar ba.

DUBA WANNAN: Kin amincewa da sakamakon zabe: Abubuwa 6 da Atiku ya fadi a jawabinsa

Kin amincewa da sakamakon zabe: Zamu gamu da Atiku a kotu - Oshiomhole
Kin amincewa da sakamakon zabe: Zamu gamu da Atiku a kotu - Oshiomhole
Asali: Depositphotos

Hakan ya sa ya ce Atiku yana da damar ya tafi kotu.

"Ba zaka hannu mutumin da ya ke tunanin an cuce shi ba zuwa kotu duk ko da irin ingancin zaben kamar yadda nayi a lokacin da nayi imanin cewa an cuce ni," a cewar Oshiomhole a yayin hirar da ya yi da manema labarai a ranar Laraba a Abuja.

"Idan kana ganin baka amince da sakamakon zabe ba, abinda yafi dacewa shine ka tafi kotu.

"Saboda haka, muna sa ran gamuwa da Alhaji Atiku Abubakar a kotu kuma za a baje hujoji a faranti amma ina gargadinsa cewa mu ma za mu iya bincikar hujojojin da za a gabatar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel