Zaben 2019: INEC ta ba mu kunya - SDP

Zaben 2019: INEC ta ba mu kunya - SDP

Dan takarar gwamna na jam'iyyar Social Democratic Party, SDP, a jihar Cross River, Eyp Ekpo ya ce bai gamsu da yadda Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC ta gudanar da zabukkan shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya ba.

Mr Ekpo ya yi wannan furucin ne a yayin wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a ranar Laraba a Calabar.

Ya ce ya kamata a ce INEC ta kware wurin shirya zabe duba da cewa hukumar ta fara shirya zaben tun 1999 zuwa 2015.

Ya ce an samu jinkiri sosai wurin rabar da kayayakin aiki kuma gashi a halin yanzu babu wanda aka hukunta saboda hakan.

DUBA WANNAN: Kin amincewa da sakamakon zabe: Abubuwa 6 da Atiku ya fadi a jawabinsa

Zaben 2019: INEC ta ba mu kunya - SDP
Zaben 2019: INEC ta ba mu kunya - SDP
Asali: Twitter

"Bai dace a 2019 ba INEC ta kasance ba ta san makamashin aiki ba duk da zabukan da tayi a baya.

"Ina son INEC ta inganta tsarin rabar da kayayakin aiki, akwai ofisoshin NIPOST a dukkan kananan hukumomin Najeriya amma ba su bukaci NIPOST su yi musu jigilar kayayakin zaben su ba.

"Kuma ba a bin dokokin zabe, mutane suna ta taimaka ma wasu wurin dangwale kuri'a sannan lokacin da aka dauka na horas da ma'aikatan wucin gadi na INEC ya yi kadan.

"Ya kamata INEC su san cewa ba za ka iya gudanar da zabe a Najeriya ba sai fa idan ka ware wasu kwanaki kayi shirin da ya dace, ya kamata su san adadin kwanakin da suke bukata.

"Bana tsamanin tsaro matsala ce, idan ka duba yadda aka gudanar da zabukan ba a samu rikici ba sosai, ina ganin 'yan sanda sun yi kokari," inji shi.

Mr Ekpo ya ce bai yi mamakin ganin yadda dan takarar jam'iyyar SDP, Donald Duke bai samu wasu kuri'u masu yawa ba saboda rikicin da aka rika yi game da tikitin takarar shugabancin kasa na jam'iyyar.

NAN ta ruwaito cewa SDP ce ta zo na uku a jihar Cross Rivers inda ta samu kuri'u 1,395, PDP ta samu 295, 737, yayin da APC ta samu kuri'u 117,302.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel