Ministan ilimi ya fitar da kididdigar adadin kudin da FG ta bawa manyan makarantu

Ministan ilimi ya fitar da kididdigar adadin kudin da FG ta bawa manyan makarantu

- Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta kashe N727,225,862,128.86 a kan yiwa makarantun gaba da sakandire hidima cikin shekaru hudu

- Gwamnati ta ce anyi amfani da kudaden ne wurin samar sabbin gine-gine, kulawa da tsaffin ayyukan, samar da kayayakin sadarwa zamani (ICT), koyar da sana'o'i, inganta dakunan karatu, horas da ma'aikata da sauransu

- Gwamnatin ta kuma ce ta ware wasu kudaden na musamman da ta baiwa manyan makarantu a dukkan shiyoyin siyasa shida na Najeriya

Adadin kudaden da gwamnati ta bawa manyan makarantu cikin shekaru hudu
Adadin kudaden da gwamnati ta bawa manyan makarantu cikin shekaru hudu
Asali: Facebook

Gwamnatin tarayya ta bawa makarantun gaba da sakandire zunzurutun kudi N727,225,862,128.86 domin gine-gine da wasu gyare-gyare masu muhimmanci ta hanyar amfani da Asusun Manyan Makarantu TETFund tsakanin 2015 zuwa 2018.

DUBA WANNAN: Kin amincewa da sakamakon zabe: Abubuwa 6 da Atiku ya fadi a jawabinsa

Ministan Ilimi, Adamu Adamu ya ce an kashe kudaden ne wurin samar sabbin gine-gine, kulawa da wasu tsaffin ayyukan, samar da kayayakin aiki da na'urorin sadarwa zamani (ICT), koyar da sana'o'i, inganta dakunan karatu, horas da ma'aikata, bincike da wasu manya-manyan ayyuka.

Baya ga TETFund, makarantun na gaba da sakandare suna samun kudade daga harajin da suke karba a makarantu da ma wasu hanyoyin na daban.

Gwamnati kuma ta ware wasu kudade na musamman da ta baiwa manyan makarantun gaba da sakandare a dukkan shiyoyin siyasa shida da ake da su a kasar kana gwamnatin ta kuma bawa Jami'ar Sojoji na Biu da ke jihar Borno wani kudi na musamman.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel