Yanzu Yanzu: Yan sanda sun tarwatsa taron manema labarai a Lagas

Yanzu Yanzu: Yan sanda sun tarwatsa taron manema labarai a Lagas

Jami’an an sanda a jihar Lagas sun hargitsa filin wani taron manema labarai a jihar, jaridar New Telegraph ta ruwaito.

Wata kungiya mai suna Orange Movement for a Free Lagos State ce ta shirya taron manema labaran wanda ya gudana a Lagos Airport Hotel da ke Ikeja.

Jagororin kungiyar sun hada da tsohon shgaaban kungiyar lauyoyin Najeriya, Olisa Agbakoba, kakakin kungiyar Afenifere, Mista Yinka 0dumakin da Sanata Tokuno Afikuyomi, wani jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Yanzu Yanzu: Yan sanda sun tarwatsa taron manema labarai a Lagas
Yanzu Yanzu: Yan sanda sun tarwatsa taron manema labarai a Lagas
Asali: UGC

Yayinda wasu daga cikin mahalartan taron suka zauna a cikin dakin taron na Oranmiyan Hall, jami’an yan sanda sun hana sauran mutane shiga otel din.

Jami’an yan sanda sun hana kowa shiga dakin taron.

KU KARANTA KUMA: Hukumar INEC na cikin ganawa don sake duba zaben shugaban kasa

Ana cikin haka sai jami’an yan sandan suka yi harbi so da dama domin tarwatsa dandazon mutanen inda kowa ke neman mafaka a harabar wurin.

Ba a san dalilin da yasa jami’an yan sandan cikin kimanin motoci 10 suka kai farmaki wajen taron ba, amma majiyoyi sun bayyana cewa hakan yunkuri ne na hanan taron gudana.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel