Minista ya kaddamar da wani katafaren aiki a garin Buhari kwanaki kadan bayan yaci zabe

Minista ya kaddamar da wani katafaren aiki a garin Buhari kwanaki kadan bayan yaci zabe

Ministan al’amuran wasanni da harkokin matasa, Solomon Dalung ya kaddamar da filin wasa da motsa jiki a garin Daura, mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda zata dauki mutane dubu uku a lokaci daya.

Legit.ng ta ruwaito Minista Dalung yana fadin gwamnati ta gina wannan filin wasa ne don ta habbaka harkar wasanni da walwalar matasa a garin Daura, asali dai akwai filin, amma ma’aikatar wasanni ta gwamnatin tarayya ta kara girmansa tare da habbakashi da kayan aiki.

KU KARANTA: An buga an barku: Daďadďun Sanatoci 10 da zasu sake komawa majalisar dattawa

Minista ya kaddamar da wani katafaren aiki a garin Buhari kwanaki kadan bayan yaci zabe
Filin
Asali: Facebook

Ministan yace a yanzu sun habbaka filin wasan da sassan buga wasu wasannin motsa jiki baya da kwallon kafa, daga cikin wasanni akwai kwallon kwando, badminton, tenis, da dai sauransu, haka zalika an gina makewayi, wajen shakatawa da dakunan sauya kaya a ciki.

A jawabinsa, Minsita Dalung ya bayyana cewa a yanzu muhimmancin wasanni bai tsaya ta wajen nishadi kawai ba, a’a, ya zarce haka domin kuwa ya zama babbar hanyar samun kudi, samar ma matasa aikin yi, hada kan al’umma da kuma kulla alakar diflomasiyya.

Minista ya kaddamar da wani katafaren aiki a garin Buhari kwanaki kadan bayan yaci zabe
Filin
Asali: UGC

Shima a nasa jawabin, gwamnan jahar Katsina, Aminu Bello Masari ya jinjina ma namijin kokarin da ministan yayi na inganta filin wasan, inda yace hakan ya nuna cewa gwamnatin tarayya na da burin ciyar da duk wani lamari daya shafi matasa gaba.

Daga karshe Gwamna Masari yayi kira ga matasa dasu tabbata sun nuna bajinta a duk abinda suka daura kansu akai, gwamnati kuma zata basu tallafin daya dace, sa’annan yayi alkawarin gwamnatin jahar za ta dauki ragamar kulawa da filin.

Minista ya kaddamar da wani katafaren aiki a garin Buhari kwanaki kadan bayan yaci zabe
Filin
Asali: Facebook

Daga cikin wadanda suka halarci bikin kaddamar da filin wasan akwai mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk da yan majalisarsa, kwamishinoni, manyan jami’a gwamnati, yan siyasa da kuma kungiyoyin matasa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel