Jam’iyyar APC ta yi amfani da jami’an tsaro wajen razana yan PDP - Tambuwal

Jam’iyyar APC ta yi amfani da jami’an tsaro wajen razana yan PDP - Tambuwal

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewar jam’iyya mai mulki ta APC ta yi amfani da jami’an tsaro wajen razana magoya bayan PDP a kokarin ganin sun lashe zaben da ya gudana a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu.

Tambuwal ya ce jam’iyyar APC ta hango faduwa a zabe makwanni uku kafin zabe, a sakamakon hakan ne suka fito da abubuwa da dama a a yayin gudanar da zabe domin ganin sun kai ga nasara.

Gwamnan ya kuma bayyana cewar ba a kai kayan zabe cikin lokaci ba a rumfunan zaben da jam’iyyar PDP take da matukar karfi, an kuma samu matsalar zirga-zirga wanda hakan ya sa ba a fara zabe cikin lokaci ba.

Jam’iyyar APC ta yi amfani da jami’an tsaro wajen razana yan PDP - Tambuwal
Jam’iyyar APC ta yi amfani da jami’an tsaro wajen razana yan PDP - Tambuwal
Asali: Depositphotos

A zaben jam’iyyar APC ta yi nasarar lashe kujerun Majalisar Dattawa uku da na Majalisar Wakilai bakwai a yayin da PDP ta samu Majalisar Wakilai biyu, an kuma bayyana zaben kujera daya a matsayin wanda ba a kammala zabe ba a Mazabar Bodina/Dange-Shuni/Tureta.

KU KARANTA KUMA: Aliko Dangote ne na 64 a masu kudin duniya a yanzu (jerin sunayen biloniyan)

Gwamna Tambuwal ya kuma yi kira ga magoya bayansa da su fito zaben Gwamna da na ‘Yan Majalisar Jiha da ke tafe wanda ke da matukar muhimmanci ya kuma ce ka da jama’a su razana ko su bari a tsoratar da su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel