An buga an barku: Daďadďun Sanatoci 10 da zasu sake komawa majalisar dattawa

An buga an barku: Daďadďun Sanatoci 10 da zasu sake komawa majalisar dattawa

An yi zabe an gama, sai dai don gudun kada ayi tuya a manta da albasa yasa muka dauko bayanai game da yadda zaman majalisar dattawa ta Tara za ta kasance musamman game da dadewar wasu Sanatoci suka dauka ana bugawa dasu a majalisar.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a yanzu haka akwai Sanatoci akalla guda goma cikin Sanatoci dari da tara da majalisar ta kunsa, wadanda suka kwashe sama da shekaru takwas takwas a majalisar, kuma a yanzu haka sun sake lashe zabe don cigaba da fafatawa a majalisar.

KU KARANTA: Yaki da rashawa: Sabbin Sanatoci 12 da zasu shiga majalisa tare da guntun kashi a gindinsu

Daga cikin Sanatocin nan akwai:

Ike Ekweremadu: Mataimakin shugaban majalisar dattawa tun daga shekarar 2007, wanda ya sake lashe zabe a matsayin dan majalisa mai wakiltar mazabar Enugu ta yamma a majalisar dattawa a inuwar jam’iyyar PDP karo na biyar. Tun a shekarar 2003 jama’ansa suka fara zabansa.

James Manager: Dan majalisa daga jahar Delta wanda ya sake lashe zabe a matsayin dan majalisa mai wakiltar mazabar Delta ta kudu a majalisar dattawa a inuwar jam’iyyar PDP karo na biyar. Tun a shekarar 2003 jama’ansa suka fara zabansa.

Kabiru Gaya: Tsohon gwamnan jahar Kano, wanda ya sake lashe zabe a matsayin dan majalisa mai wakiltar mazabar Kano ta kudu a majalisar dattawa a inuwar jam’iyyar APC karo na hudu. Tun a shekarar 2007 jama’ansa suka fara zabansa a inuwar jam’iyyar ANPP.

Ahmed Lawan: Jagoran masu rinjaye, wanda ya sake lashe zabe a matsayin dan majalisa mai wakiltar mazabar Yobe ta Arewa a majalisar dattawa a inuwar jam’iyyar APC karo na hudu. Tun a shekarar 2007 jama’ansa suka fara zabansa.

Oluremi Tinubu: Uwargidar jagoran jam’iyyar APC, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu wanda ya sake lashe zabe a matsayin dan majalisa mai wakiltar mazabar Legas ta tsakiya a majalisar dattawa a inuwar jam’iyyar APC karo na uku. Tun a shekarar 2011 jama’anta suka fara zabanta.

Ajari Boroffice: Sanata daga jahar Ondo wanda ya sake lashe zabe a matsayin dan majalisa mai wakiltar mazabar Ondo ta Arewa a majalisar dattawa a inuwar jam’iyyar APC karo na uku. Tun a shekarar 2011 jama’ansa suka fara zabansa a inuwar jam’iyyar LP.

Ali Ndume: Tsohon shugaban masu rinjaye wanda ya sake lashe zabe a matsayin dan majalisa mai wakiltar mazabar Borno ta kudu a majalisar dattawa a inuwar jam’iyyar APC karo na uku. Tun a shekarar 2011 jama’ansa suka fara zabansa.

Danjuma Goje: Tsohon gwamnan jahar Gombe wanda ya sake lashe zabe a matsayin dan majalisa mai wakiltar mazabar Gombe ta tsakiya a majalisar dattawa a inuwar jam’iyyar APC karo na uku. Tun a shekarar 2011 jama’ansa suka fara zabansa a karkashin lemar PDP.

Abdullahi Adamu: Tsohon gwamnan jahar Nasarawa wanda ya sake lashe zabe a matsayin dan majalisa mai wakiltar mazabar Nassarawa ta yamma a majalisar dattawa a inuwar jam’iyyar APC karo na uku. Tun a shekarar 2011 jama’ansa suka fara zabansa a inuwar jam’iyyar PDP.

Emmnuel Bwacha: Sanata daga jahar Taraba wanda ya sake lashe zabe a matsayin dan majalisa mai wakiltar mazabar Taraba ta kudu a majalisar dattawa a inuwar jam’iyyar PDP karo na uku. Tun a shekarar 2011 jama’ansa suka fara zabansa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel