Manyan APC sun fara baiwa shugaba Buhari shawara kan nade-nade, sunce dole a sauya irin ta-jiya

Manyan APC sun fara baiwa shugaba Buhari shawara kan nade-nade, sunce dole a sauya irin ta-jiya

- Daya daga cikin jiga jigan jam'iyyar APC ya shawarci shugaba Buhari da ya canza duk ministan da bai yi aiki ba

- Ya kara da shawartar shugaban da kada kada ya zabi yan uwa da abokan arziki

- Akwai korafe korafe da dama a wancan karon daga gwamnoni da kuma shuwagabannin jam'iyyar akan rashin shawartar su yayi nada ministocin

Manyan APC sun fara baiwa shugaba Buhari shawara kan nade-nade, sunce dole a sauya irin ta-jiya
Manyan APC sun fara baiwa shugaba Buhari shawara kan nade-nade, sunce dole a sauya irin ta-jiya
Asali: Twitter

Wani jigon APC na jihar Jigawa, Alhaji Ishaq Hadejia, ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da kada ya kara zabar duk ministocin da basu yi aiyukan su da ya dace ba a gwamnatin da ta gabata.

Ya kara shawartar shugaban da ya guji zabar yan uwa da abokan arziki a mulkin shi karo na biyu.

Hadejia ya bada shawarwarin ne a yayin da ya tattauna da ofishin dillancin labarai a Dutse a ranar alhamis.

GA WANNAN: Jamiyyar APC tayi babban rashi bayan da aka kada Sanatan ta a jihar sa ta Benue

Yace saboda yarda da kuma tabbacin da talakawa kewa Buhari ne yasa suka suka sake zabar shi a karo na biyu.

"Idan muka duba hakan, duk ministan da bashi da yardar mutane toh kada shugaban kasa ya kara zabar shi don tafiya zuwa mataki na gaba,"

"Wasu daga cikin ministocin basa aikin au kuma sun ware kansu, wasu ko yakin neman zabe basu maida hankali anyi dasu ba. Yanzu toh da talakawa suka sake zaben shugaban kasa Buhari, kawai ya gujewa sake zaben yan uwa da abokan arziki wajen sabuwar tafiyar."

Shugaban APCn ya kara da shawartar shugaban kasar da ya dinga tambayar gwamoni kafin zaben ministoci.

"Zan iya cewa akwai korafe korafe daga gwamnonin jihohi hadi da shuwagabannin jam'iyyar akan cewa ba a shawarce su ba yayin nada ministoci." Cewar Hadejia.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel