An samu matsala: Manyan kwamishinoni a hukumar INEC zasu yi murabus

An samu matsala: Manyan kwamishinoni a hukumar INEC zasu yi murabus

- Akwai alamun cewa wasu kwamishinonin zabe ma jiha da kwamishinonin zabe na kasa daga hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) za su yi murabus daga matsayinsu

- Hakan ya biyo bayan zargin cewa rayuwarsu na cikin hatsari sannan cewa basu samu nagartaccen tsaro a daga hukumomin tsaro

- Suna tsoron kada a kai masu mumunan hari a zaben gwamnoni da na yan majalisar jiha da zai gudana a ranar Asabar, 9 ga watan Maris

Akwai alamun cewa wasu kwamishinonin zabe ma jiha da kwamishinonin zabe na kasa daga hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) za su yi murabus daga matsayinsu biyo bayan zargin barazana da tozarci da kuma barazanar da rayuwarsu ta samu daga hukumomin tsaro a lokacin zaben Shugaban kasa da na majalisa da ya gudana a ranar 23 ga watan Fabrairu.

Kwamishinonin zabe na jiha da na kasa sun yi zargin cewa sun kasance masu dakiya da duba ga Shugaban hukumar kan tarin hatsarin da rayuwarsu ke ciki sai dai sun kasa hakan saboda shima kansa yana fuskantar tarin matsi da yawan hare-hare daga manyan mutane.

An samu matsala: Manyan kwamishinoni a hukumar INEC zasu yi murabus
An samu matsala: Manyan kwamishinoni a hukumar INEC zasu yi murabus
Asali: Original

An tattaro cewa wasu jami’an zabe na jiha da kasa na cikin tsoron cewa ana iya kai masu mumunan hari a ranar 9 ga watan Maris yayinda za a gudanar da zaben gwamna da na majalisar jiha.

Wasu majiyoyi kusa da kwamishinonin zaben sun yi ikirarin cewa an yi garkuwa da wasu jami’an zabe a lokacin zaben sannan harma aka barsu day an iska yayinda jami’an tsaron da aka ajiye domin su basu kariya suka bace, sannan suka basu a lokacin da suke tsananin bukatar su.

KU KARANTA KUMA: Jarumar Kannywood, Sadiya Kabala ta fashe da kukan murna kan nasarar Buhari (bidiyo)

Majiyoyin sun kuma zargi hukumomin tsaro, ciki harda rundunar soji da sauran hukumomi da jan hankalin jami’an zabe yayinda suke ikirarin basu kariya sannan a lokaci guda suke rarraba kayayyakin zabe ba bias ka’ida ba ga yan siyasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel