Kungiya mafi girma a Najeriya ta Igbo zalla, sun fito sun taya shugaba Buhari lashe zabe

Kungiya mafi girma a Najeriya ta Igbo zalla, sun fito sun taya shugaba Buhari lashe zabe

- Kungiyar Igbo ta Ohanaeze Ndigbo, sun taya shugaban kasa murnar lashe zabe

- Kungiyar tace Buhari ya cancanci samun wannan nasara

- A zaben wannan karon yan kabilar ta Igbo sun fito sun kadawa Buhari kuri'ar su sama da shekara ta 2015

Kungiya maffi girma a Najeriya ta Igbo zalla, sun fito sun taya shugaba Buhari lashe zabe
Kungiya maffi girma a Najeriya ta Igbo zalla, sun fito sun taya shugaba Buhari lashe zabe
Asali: UGC

Kungiyar Igbo mafi girma a al'adunsu, Ohanaeze Ndigbo, ta fito karara ta taya shugaban kasa murnar lashe zabe da yayi a karo na Biyu.

Sakataren kungiyar Uche Ukwukwu ne ya bayyana hakan a yayin gudanar da wani taro a Enugu a ranar Alhamis inda yace Buhari ya cancanci samun wannan nasara.

Yace "Ohanaeze Ndigbo sun nuna tsantsar farin cikin su da kuma taya murnar su ga shugaban kasa Muhammad Buhari bisa ga wannan nasara daya samu a zaben daya gudana a ranar Asabar 23 ga watan Fabrairu shekara ta 2019,ya samu wannan nasara ne sanadiyyar dumbin kuri'u daya samu wanda hakan ke nuni da cewa shugaban kasar yayi abinda ya kamata a shekaru 4 da suka gabata".

GA WANNAN: Yaki na iya barkewa tsakanin kasashen Indiya da Pakistan, kasashe masu makaman Nukiliya

"Ndigbo suna kara farin ciki bisa ga kuri'un da suka kada masa sama da wanda suka kada a shekara ta 2015, sunyi kira ga yan Najeriya dasu karbi wannan sakamako da hannu bibbiyu".

Daga karshe ya kara da cewa nan bada jimawa ba zasu kaiwa shugaban kasar ziyarar taya murna sannan kuma su bayyana masa bukatun su.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel