Dan takarar PDP da Atiku ke so ya baiwa jihar Adamawa na so yafi Bondow iya biyan mafi karancin albashi

Dan takarar PDP da Atiku ke so ya baiwa jihar Adamawa na so yafi Bondow iya biyan mafi karancin albashi

- Dan takarar gwamna a jam'iyar PDP a jihar Adamawa yayi alkawarin mafi karancin albashi N32,000 idn har ya samu nasara

- Yace farin cikin ma'aikata yana daga cikin tsare-tsaren sa guda 11

- Yace zai tabbatar da wannan abu cikin awanni 48 da shigar sa office

Dan takarar PDP da Atiku ke so ya baiwa jihar Adamawa na so yafi Bondow iya biyan albashi
Dan takarar PDP da Atiku ke so ya baiwa jihar Adamawa na so yafi Bondow iya biyan albashi
Asali: Twitter

Dan takarar gwamna a jam'iyar PDP a jihar Adamawa Alhaji Umaru Fintiri yayi alkawarin maida mafi karancin albashi zai koma N32,000 matukar aka zabe shi a ranar Asabar 9 ga watan March.

Fintiri ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da yake tattaunawa da ma'aikata a Yola.

Yace walwalar ma'aikata yana daya daga cikin tsare-tsaren sa guda 11.

"Jihar Adamawa jiha ce ta ma'aikata dake bukatar gwamnan dazai tsaya musu tsayin daka".

GA WANNAN: Yaki na iya barkewa tsakanin kasashen Indiya da Pakistan, kasashe masu makaman Nukiliya

"Zan tabbatar da wannan abu cikin awanni 48 da shiga office".

Da yake tofa albarkacin bakin sa a wajen taro ciyaman na NLC a jihar Mr Jeremiah Ngwakwar ya mika godiyar sa ga Fintiri bisa sannan taro sannan ya shawarci ragowar yan takarar dasu sanya walwalar ma'aikata sama da komai.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel