Jarumar Kannywood, Sadiya Kabala ta fashe da kukan murna kan nasarar Buhari (bidiyo)

Jarumar Kannywood, Sadiya Kabala ta fashe da kukan murna kan nasarar Buhari (bidiyo)

Yan Najeriya daga bangarori daban-daban na ci gaba da martini akan nasarar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a zaben Shugaban kasa da ya gudana a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu.

Yayinda wasu ke murnar nasarar da Shugaban kasar ya samu wasu sun nuna bakin ciki akan tazarcen Shugaban Najeriyan.

Legit.ng ta tattaro cewa daya daga cikin magoya bayan Shugaban kasar kuma jarumar Kannywood, Sadiya Kabala ta je shafin zumunta inda ta nuna farin ciki yayinda ta fashe da kukan murna akan nasarar da Shugaban kasar ya samu a zaben.

A bidiyon wanda kakakin kungiyar kamfen din Shugaban kasa na APC, Festus Keyamo (SAN) ya wallafa , an gano Sadiya tana yiwa Buhari barka da samun nasara sannan ta yi godiya ga Allah da ya ba Shugaban kasar Nasara yayinda take hawaye idanu bibbiyu.

Kalli bidiyon a kasa:

KU KARANTA KUMA: Zaben Shugaban kasa: Obasanjo yayi tsit akan nasarar Buhari

A baya mun ji cewa shahararren dan was an nan na Kannywood kuma mawakin zamani, Adam A Zango ya taya Shugaban kasa Muhammadu Buhari murnar lashe zaben Shugaban kasa a karo na biyu a zaben da ya gudana a ranar Asabar da ya gabata.

A wani dan gajeran bidiyo da jarumin ya wallafa a shafinsa na Facebook ya nuna farin ciki akan nasarar da Shugaban kasar yayi inda har ya ajiye lemun kwalba a gabansa domin bikin wannan nasara.

Hakan na zuwa ne dai bayan jarumin ya bar tafiyar Baba Buhari inda ya koma tafiyar Atiku Abubakar dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel