Zaben Shugaban kasa: Obasanjo yayi tsit akan nasarar Buhari

Zaben Shugaban kasa: Obasanjo yayi tsit akan nasarar Buhari

Yayinda ake ci gaba da zuba rowan taya murna daga ciki da wajen kasar akan nasarar zarcewa da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi, tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo yayi tsit aan lamarin.

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) Farfesa Mahmood Yakubu a safiyar ranar Laraba, 27 ga watan Fabrairu ya kaddamar da Shugaba Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben ranar Asabar.

Manyan yan Najeriya da masu fada aji harma da shugabannin duniya sun yaba tare da taya Buari murnar nasarar da yayi a zaben, wanda aka yi cikin lumana kuma sahihi.

Zaben Shugaban kasa: Obasanjo yayi tsit akan nasarar Buhari
Zaben Shugaban kasa: Obasanjo yayi tsit akan nasarar Buhari
Asali: Depositphotos

San gashi an nemi Obasanjo wanda ya dunga tofa albarkacin bakinsa a lokacin zaben an rasa yayinda yayi gum da bakinsa akan lamarin tun bayan da aka sanar da sakamakon zaben.

Wakilin kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya nemi kakakin Obasanjo, Kehinde Akinyemi a waya sai dai yaki daukar wayar yayinda yaki amsa sakon tambayoyi da aka aika masa ta text.

KU KARANTA KUMA: Sakamakon Zabe: PDP na shirin tayar da bore a Najeriya

NAN ta tuna cewa so da dama Obasanjo ya caccaki Buhari a bainar jama’a sannan ya nuna adawa dashi yan watanni kafin zabe.

Tsohon Shugaban kasar ya mara wa Atiku Abubakar, dan takarar Shugaban kasa a babbar jam’ iyyar adawa Peoples Democratic Party (PDP) baya, bayan ya taba zargin sa da aikata rashawa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel